‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Abubuwan Fashewa A Katsina

[ad_1]

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta kama mutane uku bisa zargin mallakar abubuwan fashewa ba bisa ƙa’ida ba.

An kama su ne a cikin wata mota ƙirar Golf a ƙauyen Koza da ke ƙaramar hukumar Daura.

  • Jihohin Nijeriya 5 Da Matsalar Tsaro Ta Fi Ƙamari A 2025 — Rahoto
  • Ƴan Boko Haram Sun Nemi Dalar Amurka $300,000 Domin Sakin Mutane Biyu

‘Yansanda sun ce kamen ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2026, yayin wani bincike da suka gudanar bisa bayanan sirri.

A cikin motar, jami’an tsaro sun gano dubban abubuwan fashewa da aka ɓoye.

Bincike ya kai ga kama wasu ƙarin mutane biyu da ke da alaƙa da lamarin.

Gaba ɗaya, ‘yansanda sun ƙwato abubuwan fashewar guda kusan 7,500 da kuma buhun gelatine sama da 30 masu nauyin sama da kilo 2,200.

Waɗanda ake zargin sun amsa laifin, kuma rundunar ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Har yanzu ana ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *