’Yan sanda sun ceto mutum 3, sun kama wasu 6 kan zargin satar mutane a Nasarawa
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta ceto mutum uku da aka sace tare da kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata laifin.
An gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ’yan banga da ke yankin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce waɗanda aka ceto sun haɗa da mata biyu da namiji ɗaya.
An sace su ne a ƙauyen Angara da ke Ƙaramar Hukumar Lafia.
Ya ce an ceto su cikin ƙoshin lafiya ba tare da sun ji rauni ba.
A cewarsa, mutanen da ake zargi da sace su, sun amsa cewa su ne suka aikata laifin.
An miƙa su zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
SP Nansel, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga sashen Assakio ne suka gudanar da aikin bayan sun karɓi ƙorafi a ranar 7 ga watan Janairu, 2026.
“Wannan aiki ya biyo bayan wani ƙorafi da aka shigar a ranar 07 ga watan Janairu, 2026, inda aka bayar da rahoton cewa wasu da ake zargin wasu masu satar mutane ne sun kai hari ƙauyen Angara suka tare da sace mata biyu.
“Sun bar jariri a wajen, daga bisani kuma suka sake sace wani namiji a ƙauyen,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bayan samun wannan bayani, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, nan take ya bayar da umarnin farautar masu laifin.
“Bisa wannan bayani, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci jami’an tsaro da su fara farautar waɗanda suka aikata laifin.
“Hakan ya kai ga kama mutanen da ake zargi tare da ceto waɗanda aka sace,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma tabbatar wa mazauna Jihar Nasarawa cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da aikata laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link