Tinubu ya taya Abba murnar cika shekaru 63 a duniya




Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekaru 63 a duniya.

Shugaban Tinubu, ya kuma yaba wa Gwamnan kan yin gaskiya da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima.

Wannan na cikin wani saƙon taya murna da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.

Shugaban ƙasar ya ce kyawawan halayen Gwamna Abba sun bayyana yadda yake tafiyar da al’amuran Jihar Kano tun bayan hawansa mulki.

Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa tun da Abba ya hau mulki a 2023, ya mayar da hankali wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da jin daɗin talakawa.

Ya kuma tunatar da cewa Gwamna Abba ya taɓa zama Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri daga shekarar 2011 zuwa 2015 a ƙarƙashin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ya ce wannan ƙwarewa ta ba shi damar gudanar da manyan ayyukan ci gaba a Kano.

Shugaban ƙasar, ya ce gwamnatin Abba ta samar da ci gaban siyasa a Kano, tare da manufofi da ke kare muradun talakawa, bisa tafarkin marigayi Malam Aminu Kano.

A cewarsa, ƙwarewar da Abba ya samu a baya ta taimaka masa wajen aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa a jihar, ciki har da shirye-shiryen sabunta birane, gina gadoji da hanyoyi, da kuma aikin tituna masu tsawon kilomita biyar a faɗin ƙananan hukumomin jihar.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba da yadda gwamnan ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, inda ya ce hakan ya hakan ya bai ɗaliban Kano kyakkyawan sakamako a jarabawar NECO.

Shugaba Tinubu, ya yi wa Gwamna Abba fatan tsawon rai, lafiya, da ƙarin shekaru masu cike da tasiri da sauyi a jagoranci a Jihar Kano.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *