Me Ya Faru Bayan Harin Sojin Amurka A Nijeriya?

[ad_1]

Ƙurar da ta taso tun bayan zargin ikirarin kisan gillar Kiristoci a Nijeriya, wanda shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya zargi gwamnatin Nijeriya da yin sakaci ga hare-haren da ake kai wa Kiristoci inda ya yi barazanar dakatar da tallafin Amurka ga Nijeriya da kuma yiwuwar kaddamar da matakin soja don “kawar da” ‘yan ta’adda da ke da alhakin kisan.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da wasu masu faɗa aji a ƙasar, da suka haɗa da shugabannin Siyasa da Malaman Addinin Musulunci, cikin gaggawa suka fara mayar da martani ga shugaban na Amurka kan ikirarin da ya yi.

  • Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi
  • Sauya Sheka: Gwamna Abba Ya Yi Daidai

Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan harkokin rashin fahimtar juna, Daniel Bwala, da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.

A nasa martanin, Jagoran Siyasa, Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bayyana cewa, “Ya kamata a fahimci cewa Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ikon kanta. Matsalolin tsaro da muke fuskanta ba su da alaƙa da addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa. ‘Yan bindigar da ke addabar mu suna cutar da ‘yan ƙasa ne duka ba tare da bambancewa ba.”

Don haka, ya shawarci gwamnatin Amurka da ta daina yin barazana, maimakon haka ta taimaka wa Nijeriya da kayan zamani don magance matsalolin tsaro da ake fama da su.

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, shi ma a nasa martanin, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa kan shugaban Amurka, Donald Trump, bayan barazanar da ya yi na kawo hari Nijeriya.

Gumi ya kuma shawarci gwamnatin Tarayya da ta kira Jakadan Amurka domin neman janye wannan barazana, tare da gargaɗin cewa idan hakan bai faru ba, Nijeriya ta yanke hulɗar diflomasiyya da Amurka.

Biyo bayan haka ne, tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ofishin mai ba da shawara ga shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bazama kasar Amurka, inda ya gana da Sakataren Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, a Washington.

Duk da kiraye-kiraye da ‘yan Nijeriya suka yi kan tabbatar da cewa, iƙirarin Shugaba Trump kan kisan kiyashi ga Kiristoci a ƙasar ba haka ba ne, kowane ɓangare na ɗanɗana kuɗarsa, amma sai da Amurka ta kawo harin makami mai linzami a wasu yankunan ƙasar.

Hare-haren sama da Sojojin Amurka suka kai a Arewa maso Yammacin Nijeriya sun samu martani daga wani ɗan Majalisar Wakilan Amurka, Riley Moore, wanda ya bayyana su a matsayin mataki na farko na kawo ƙarshen kisan jama’a da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.

Moore ya ce hare-haren, da aka aiwatar tare da haɗin gwuiwar Gwamnatin Nijeriya, na da nufin dakatar da ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci, yana mai cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana ƙudurinsa na ganin an kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Nijeriya.

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya tabbatar da cewa aikin ya gudana ne da goyon bayan Nijeriya, yayin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce hare-haren na cikin tsarin haɗin gwuiwar tsaro da ƙasashen waje don yaƙi da ta’addanci.

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa harin saman da Amurka ta kai a ranar Alhamis a Nijeriya an yi su ne da cikakken sani, da goyon baya bayan samun bayanan sirri, da kuma sahalewar Gwamnatin Tarayya.

Tuggar ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce hukumomin Nijeriya sun kasance cikin tattaunawa kai tsaye da Amurka kafin a aiwatar da harin. Ya ce, ya tattauna da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, na tsawon mintuna 19 kafin harin, sannan kuma mintuna biyar kafin a kai harin.

Bayan harin saman da rundunar Sojin Amurka ta kai a ranar Kirsimeti a Arewacin Nijeriya, hukumomin soja a Jihar Sokoto sun yi kira ga mazauna jihar da su mika duk wani ragowar bam ko wani baraguzan abubuwan fashewa da suka samu daga wuraren harin.

Harin saman, wanda aka kai daga daren 25 ga Disamba zuwa safiyar 26 ga Disamba, 2025, ya mayar da hankali ne kan sansanonin ‘yan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar ISWAP a dajin Bauni.

Duk da tabbacin cewa babu farar hula da suka rasa rayuka, ragowar kayan fashewa da abubuwan da ba a tantance ba da suka faɗo kusa da yankin sun haifar da damuwa kan tsaro. Sojojin sun yi kira ga mazauna yankin da su hanzarta miƙa duk wani ragowar bam ko kayan da suka ɗauka ga hukumomin tsaro don kauce wa fashewar haɗari da kuma taimakawa wajen cikakken bincike na ɓarnar da aka yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *