Gwamnatin Tarayya Ta Kudiri Aniyar Bunkasa Sana’ar Kiwon Dabbobi Ta Mata —Minista


Daga Abubakar Abba

Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, ya sanar da cewa; gwamnatin tarayya ta sanya kudurinta, wajen bunkasa kiwon dabbobi da matan kasar ke yi.

Ya bayyana haka ne, a hirar da aka yi da shi a Abuja, inda ya ce; mata su ne kashin bayan habaka fannin tattalin arzikin kiwon dabbobi a fadin kasar.

  • NNPP Ta Rushe Shugabancinta A Kano Biyo Bayan Jita-jitar Sauya Sheƙar Abba Zuwa APC
  • Batutuwan Da Suka Ci Wa ‘Yan Adawa Tuwo A Ƙwarya A Siyasar 2025

A cewar ministan, a karkashin shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnatinsa ta daga darajar fannin kiwon dabbobi na kasa da kuma kara samar da dama kan sana’o’in da matan kasar ke gudanarwa, musamman domin matan su bayar da tasu gudanmawar ga fannin na kiwon dabbobi.

Ya kuma yaba wa matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, kan ci gaba da tallafa wa matan kasar da ta ke yi.

Maiha ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa, ba a bar matan kasar a baya ba, wajen gudunmawar da suke ci gaba da bayarwa na habaka tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa, ma’aikatarsa za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da aikin kungiyar ta AWARFA-N da kuma sauran abokan hadaka, domin kara samar da wata damar a fannin kiwon Zuma da kiwon Akuyoyi da samar da madarar Shanu da kuma kiwon Kajin gidan gona, musamman domin samun riba.

A nata jawabin tun da farko, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar ta Kiwon, Chinyere Ijeoma Akujobi, ta bayyana cewa; matan kasar na ci gaba da bayar da gudunmawarsu a fannin aikin noma da samar da abinci mai gina jiki da kuma samar da kasuwar da ta dace a daukacin fadin kasar.

Ta sanar da cewa, tsarin da aka samar na kasa don kara bunkasa kiwon dabbobi, ya mayar da hankali ne ga mata da kuma matasan kasar.

A cewarta, za a kuma gudanar da taron a nan gaba; wanda a karkashin shirin bunkasa kiwo na fadar shugaban kasa, zai mayar da hankali ne ga mata da kuma matasa.

A cewarta, a karkashin shirin, za a samar da dubban ayyukan yi a kananan hukumomi 774 na kasar.

Ita kuwa, Bictoria Madedor a wajen taron, ta gabatar da aikin na kungiyar AWARFA-N na bunkasa kiwon dabbobi, har na tsawon shekaru biyar.

Ta bayyana cewa, nufin kungiyar shi ne, ci gaba da taimaka wa mata, musamman domin su zama a kan gaba wajen zuba jari da samar da sana’o’i a fannin kiwon dabbobi.

Ta kara da cewa, samar da wadatattun kudade da bunkasa fannin kiwon, domin samun riba da samar da kayan aikin kiwo na zamani, su ne mayan ginshikan da kungiyar ta mayar da hankali a kansu daga 2025 zuwa 2029.

Ita ma a sakonta na fatan alheri a wajen taron, Sarah Ossiya, wadda ta fito daga kungiyar AU-IBAR, kira ta yi da a mayar da hankali wajen kara sanya mata a cikin fannin kiwon dabbobi a kasar nan.

Ta bayyana cewa, Afirka ta yi asarar kusan kashi goma a fannin tattalin arziki, musamman wajen gaza samar da abinci mai gina jiki ga al’ummar da ke yankin, inda ta kara da cewa; samar da abinci mai gina jiki ga dabbobi, tamkar samar da shi ne ga sauran bil Adama.

Ta bukaci samar da sauye-sauye a bangaren samar da wadatattun kudade da kuma kara samar da kasar yin noma, musamman domin amfanin matan kasar da ke gudanar da kiwon dabbobi.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *