Shugaban mulkin sojan Guinea, Doumbouya, ya lashe zaben Shugaban Ƙasar

[ad_1]



Shugaban mulkin soja na ƙasar Guinea, Mamady Doumbouya, ya lashe zaɓen shugaban kasar da kaso 86.72 cikin 100.

Wannan dai shi ne zaben farko da ƙasar ta gudanar tun bayan juyin mulkin sojoji na shekarar 2021.

Sakamakon da aka sanar a ranar Talata ya nuna Doumbouya ya samu nasarar ce a zaɓen ranar 28 ga Disamba, wanda ya ba shi rinjaye kai tsaye ba tare da bukatar zagaye na biyu ba.

Kotun Kolin ƙasar na da kwanaki takwas domin tabbatar da sakamakon idan aka samu ƙalubale.

Ana ganin wannan zabe a matsayin hanyar tabbatar da mulkin Doumbouya a matsayin shugaban kasa.

Haka kuma, zaben ya kawo ƙarshe sauya tsarin mulkin ƙasar daga na soja zuwa farar hula da aka fara shekaru hudu da suka gabata bayan Doumbouya ya kifar da tsohon shugaban kasa Alpha Conde, wanda ya rike mulki tun daga 2010.

Masu suka sun ce tun bayan juyin mulkin, Doumbouya ya daƙile ’yan adawa da masu sukar gwamnati, lamarin da ya bar shi ba tare da manyan abokan hamayya ba daga cikin sauran ‘yan takara guda takwas da suka shiga zaben.

Har yanzu dai Alpha Conde da tsohon jagoran adawar ƙasar na tsawon lokaci, Cellou Dalein Diallo, suna rayuwa a matsayin ’yan gudun hijira a wasu ƙasashen.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *