An Kaddamar Da Cibiyar Cinikayyar Kofin Habasha A Zhuzhou Na Sin
[ad_1]
An kaddamar da cibiyar cinikayyar gahawa ko kofi na kasar Habasha, a garin Zhuzhuo na lardin Hunan dake kasar Sin, a wani mataki na baiwa Habasha damar cin gajiyar kasancewarta tushen samar da Gahawa, da baiwa kasar zarafin shiga katafariyar kasuwar kasar Sin.
Bikin kaddamar da cibiyar a hukumance wanda ya wakana a jiya Asabar, daya ne daga sakamakon farko na taron hadin gwiwar Sin da Habasha, a fannin raya tattalin arziki da cinikayyar kofi wanda ya gudana a birnin na Zhuhou.
Kazalika, taron ya shaida bunkasar alakar sassan biyu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, inda batun cinikayyar kofi ya kasance muhimmin jigon hakan. Taron ya hallara mutane kimanin 300, ciki har da jami’an gwamnatoci, da kwararru, da wakilan hukumomi, da jagororin ‘yan kasuwa na Habasha da na lardin Hunan.
Habasha na matsayin tushen samar da gahawa, kuma kasa dake kan gaba a duniya wajen fitar da Gahawa mai inganci, kuma kasar Sin ce ta hudu a duniya, cikin jerin kasashen da Habasha ta fi fitar da Gahawa zuwa kasuwanninsu.
A yayin taron, jakadan Habasha a kasar Sin Tefera Derbew Yimam, ya shaidawa kafar Xinhua cewa, sun lura da matukar karuwar masu shan kofi a kasar Sin. Kuma hakan muhimmin jigo ne dake shafar bukatar karin fitar da shi zuwa Sin. Ya kuma bayyana manufar Sin ta dagewa kasashen Afirka masu alakar diflomasiyya da ita harajin shigar da hajoji, a matsayin kyakkyawar damar inganta gogayya a babbar kasuwar Sin. Jakadan ya kuma bayyana fatan ganin ci gaba da bunkasar cinikayyar hajojin manyan fasahohi, da Sin ke kerawa a kasuwannin Habasha. (Mai fassara: Saminu)
[ad_2]
Source link