Tinubu ya sauya sunan Jami’a zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauya sunan Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, a Jihar Bauchi, zuwa sunan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalan malamin a Bauchi.
Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya, inda ya ce rayuwarsa ta kasance cike da tawali’u, hidima da sadaukarwa.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa, Ya kuma sanya shi a Aljanna Firdausi.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalan malamin, gwamnatin Jihar Bauchi da al’ummar jihar haƙurin jure wannan rashi.
Tinubu, ya ce an sauya sunan jami’ar zuwa Sheikh Dahiru Bauchi ne, domin girmama shi tare da la’akari da irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi.
Shugaban Ƙasar ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.
Da yake magana a madadin iyalan marigayin, babban ɗansa, Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa ziyarar ta’aziyyar.
Ya kuma gode shugaban bisa zuwa Bauchi da ya yi da kansa domin yi musu ta’aziyya.
Haka kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, bisa ci gaba da nuna goyon baya ga iyalan malamin.
A nasa jawabin, Gwamna Bala Muhammad ya gode wa Shugaba Tinubu bisa girmama iyalan marigayin da kuma Jihar Bauchi gaba ɗaya.