Majalisa Ta Buƙaci Sufeton ‘Yansanda Ya Binciki Kashe-kashen Rayuka a Filato
[ad_1]
Majalisar Dattawa ta umarci Sufeto Janar na ‘yansanda, Olatunji Disu, da ya kaddamar da cikakken bincike kan hare-haren kisan da aka yi kwanan nan a Anguwan Rukuba, karamar hukumar Jos ta Arewa ta Jihar Filato, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 28.
Yayin da ‘yan majalisar suka bukaci a cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya, majalisar ta kuma amince da tura wata babbar tawaga karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, domin kai ziyarar jaje ga al’ummomin da lamarin ya shafa da kuma jama’ar Jihar Filato baki daya.
- Kwankwaso Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jos, Ya Nemi Hukumomi Su Ɗauki Mataki
- Ghana Ta Sallami Kocinta Kafin Fara Gasar Kofin Duniya
Wadannan matakan sun biyo bayan kudurin da Sanata Diket Plang da kuma Sanata Dachung Mwadkon suka gabatar a ranar Talata, inda suka bayyana damuwa matuka kan tabarbarewar tsaro a kananan hukumomin Kanam da Jos ta Arewa.
A yayin jagorantar kudurin, Plang ya nuna takaicinsa cewa Jihar Filato, wadda a da ake yi wa lakabi da “Gidan Zaman Lafiya da Yawon Bude Ido,” na fuskantar sake barkewar rikice-rikice bayan shekaru na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
[ad_2]
Source link