Gwamnan Kano ya sauke Sagagi daga muƙamin Kwamishina

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shehu Wada Sagagi daga muƙaminsa na Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu.

An bayyana hakan ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a daren ranar Laraba.

Sanarwar ta ce an umarci Sagagi da ya miƙa ragamar aiki ga Daraktan Kasuwanci har sai an bayar da umarni na gaba.

Gwamna Abba ya gode wa Sagagi bisa gudunmawar da ya bayar yayin da yake riƙe da muƙamin, musamman a fannonin siyasa, addini da kuma bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i a jihar.

Haka kuma ya yi masa fatan alheri, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin samar da kyakkyawan shugabanci da ingantaccen aiki.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke yi domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.

Idan ba a manta ba wannan ne karo na biyu da aka sauke Sagagi daga majalisar gwamnatin Abba.

A watan Disamban 2024 an sauke shi daga muƙamin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *