APC Ta Musanta Zargin Aikata Cin Hanci, Ta Bai Wa NNPP Sa’o’i 72 Ta Ba Da Haƙuri
[ad_1]
Jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin da tsagin Kwankwasiyya na NNPP ya yi cewa gwamnatin Jihar Kano na tsoma baki a harkokin kotu.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Auwalu Soja Gwale, ya fitar, APC ta ce zargin ba gaskiya ba ne kuma babu hujja a kansa.
- ADC Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki El-Rufai Ko Ta Gurfanar Da Shi A Kotu
- Adadin Mayaƙan ISWAP Da Aka Kashe A Borno Ya Kai 75
Jam’iyyar ta kuma musanta rahotannin cewa an biya kuɗi domin yin tasiri a wata kotu da ke Abuja.
APC ta bai wa NNPP da kakakinta, Ibrahim Karaye, wa’adin awanni 72 su janye zargin tare da neman afuwa, ko kuma su fuskanci matakin shari’a.
APC ta ce an yi hakan ne domin ɓata sunan ɓangaren shari’a.
Ta jaddada cewa gwamnatin Jihar Kano ba ta taɓa tsoma baki a harkokin kotu ba.
Jam’iyyar ta kuma zargi ɓangaren NNPP da yawan yin irin waɗannan kalamai a duk lokacin da abubuwa ba su tafi yadda suke so ba.
Ta buƙace su da su mayar da hankali wajen magance rikice-rikicen cikin gida maimakon yin zarge-zarge marasa tushe.
[ad_2]
Source link