Isra’ila ta yi iƙirarin kashe babban jami’in tsaron Iran Ali Larijani
[ad_1]
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya sanar da cewa an kashe babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, a wani hari da suka kai a Tehran.
Sai dai zuwa yanzu babu wata sanarwa daga ɓangaren Iran da ta tabbatar ko ta ƙaryata wannan iƙirari, kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.
Rahotanni sun ce an ji ƙarar fashe-fashe masu ƙarfi a sassa daban-daban na Tehran cikin sa’o’in da suka gabata, inda hare-haren suka bazu zuwa wasu biranen ƙasar kamar Ahvaz, Isfahan da Shiraz.
Hare-haren sun kuma shafi muhimman gine-gine da cibiyoyin tsaro, ciki har da kwamandan rundunar Basij, Gholamreza Soleimani.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe Gholamreza Soleimani, wanda ke jagorantar rundunar sa-kai ta Basij ƙarƙashin rundunar juyin-juya-hali ta IRGC, a wani hari da suka kai a daren Litinin.
Sun bayyana kisan a matsayin “babban koma baya” ga tsarin jagoranci da sarrafa rundunonin Iran, tare da alƙawarin ci gaba da kai hare-hare kan manyan kwamandojin ƙasar.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce jiragen yaƙi da dama sun kai hare-hare lokaci guda a Tehran, Shiraz da Tabriz.
A cewarsu, hare-haren sun lalata cibiyoyin tsaron Iran da suka haɗa da ma’aikatar leƙen asiri da kuma sansanonin Basij, tare da kai hari wuraren adana makamai masu linzami, jiragen yaƙi marasa matuƙa da tsarin kariyar sararin samaniya.
A Shiraz kuma, an kai hari hedikwatar tsaron cikin gida da wurin adana makamai masu linzami, yayin da a Tabriz aka lalata wasu na’urorin tsaro.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link