Netanyahu ya yi wa jita-jitar mutuwarsa shaguɓe

[ad_1]



Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke bayyana cewa ya mutu, inda ya wallafa wani ɗan gajeren bidiyo yana yi wa lamarin shaguɓe.

A cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, an ga Netanyahu yana karɓar kofi a wani shagon shan shayi da ke birnin Qudus, inda ya ce cikin zolaya, ya ce “Na mutu saboda shayin kofi,” wata magana ta harshen Ibrananci da ke nufin mutum na matuƙar son wani abu.

Daga nan sai ya ɗaga hannuwansa yana tambayar masu kallo su ƙirga yatsunsa, yana mai nuni da jita-jitar da ta bazu cewa wani jawabin da ya yi a talabijin an ƙirƙire shi ne da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI, bayan wasu suka ce kamar yana da yatsu shida a hannu ɗaya.

A cikin bidiyon, Netanyahu ya kuma buƙaci ’yan Isra’ila su ci gaba da bin umarnin tsaro idan aka yi gargaɗin harin makamai masu linzami.

Ya ce juriyar da al’ummar ƙasar ke nunawa na ƙara masa ƙwarin gwiwa, ga gwamnati da rundunar soji da kuma hukumar leƙen asirin ƙasar Mossad.

“Muna aiwatar da wasu matakai da ba zan iya bayyana su a yanzu ba, amma muna kai wa Iran hari sosai, haka kuma Lebanon,” in ji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne kuma rundunar dakarun juyin juya hali ta Iran (IRGC) ta lashi takobin ci gaba da farautar Netanyahu har sai ta ga bayansa yayin da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ya shiga mako na uku.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *