Gwamnan Zamfara Dauda Dare ya koma APC

[ad_1]



Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a ƙasar.

Mataimaki kuma muƙaddashin Gwamnan, Mani Mummuni ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau.

Bayan kammala taron, mambobin majalisar zartarwa da manyan jiga-jigan PDP a jihar sun amince da komawa APC, inda aka riƙa ɗaga tutoci da rera taken jam’iyyar APC a matsayin nuna goyon baya ga sabon matakin.

Aminiya ta ruwaito cewa a halin yanzu gwamnan yana Saudiyya inda ya tafi Umrah.

Ana iya tuna cewa, Gwamna Dare ya bayyana cewa hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke kan halascin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a bara zai taimaka wajen tantance matakin da za su ɗauka dangane da rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

A halin yanzu kuma, muƙaddashin gwamnan yana ganawar sirri da ‘yan majalisar dokokin jihar domin tattauna sabon matsayar siyasar da kuma yadda za su hada kai a karkashin APC.

A wannan Litinin ɗin ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin cewa babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a bara, wanda ya ayyana Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar bai halasta ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *