DSS Ta Kama Kwamandan Ƴan Ta’addan IPOB Da Ake Zargi Da Kashe Ƴansanda

[ad_1]

Jami’an Tsaro Na DSS sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da mambobin ƙungiyar tsageru ƴan aware ne yayin wani sumame da suka kai a Jihar Enugu State.

Wadanda aka kama sun hada da Sabastine Odo Odam, wanda ake zargin kwamandan Eastern Security Network ne, da kuma Ejike Daniel, mamba na Indigenous People of Biafra. An kama su ne a garuruwan Eha-Amufu da Umuhu na ƙaramar hukumar Isi-Uzo.

  • DSS Ta Kama Wasu Jami’an Tsaro Kan Zargin Taimaka Wa El-Rufai
  • Bayan Shekaru 7, DSS Ta Sake Buɗe Binciken Ɓacewar Dadiyata

Majiyoyin tsaro sun ce an gudanar da sumamen ne ranar Juma’a bayan watanni na sa ido da tattara bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin. An ce matakin ya biyo bayan hare-hare da dama da aka kai kan ofisoshin ‘yansanda da kuma kashe-kashen da aka samu tsakanin 2024 zuwa 2026.

Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin sun amsa hannu a wasu hare-hare da aka kai kan ofisoshin ‘yansanda inda aka sace makamai, ciki har da kashe ma’aikata 11 a Fabrairu 2026 da kuma ‘yansanda da dama a lokuta daban-daban.

An ce mazauna yankin Isi-Uzo sun yi maraba da kamen jama’ar yadda jaridar Global News ta rawaito, suna fatan hakan zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya. A halin yanzu ana tsare da waɗanda ake zargin a hannun DSS, kuma ana sa ran za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *