Wane ne sabon Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khamenei?
[ad_1]
Majalisar magabata ko majalisar ƙoli ta malaman addini da ke Iran ta zaɓi Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran addinin ƙasar, inda ya maye gurbin mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a yayin harin da Amurka da Israila suka ƙaddamar a makon jiya.
Wannan lamari da ya tabbatar da cewar majalisar ta bijire wa barazanar da Amurka da Isra’ila suka yi kan naɗa sabon jagoran ba tare da sun yi ruwa da tsaki ba.
A cikin wata sanarwar da majalisar ta magabatan Iran ta fitar a jiya Lahadi, ta ce Mojtaba Khamenei mai shekaru 56, ya zama jagoran addinin ƙasar na uku a tarihi, bayan da wakilan majalisar suka kaɗa masa ƙuri’u.
Tun dai da safiyar Lahadin ce majalisar ƙoli ta malaman addini da ke da alhakin zaɓen sabon jagoran ƙasar Iran ta ce ta riga ta yanke hukunci kan wanda zai gaji kujerar, amma a lokacin ba a bayyana sunansa ba.
Mamba a cikin majalisar, Ahmad Alamolhoda, ya ce an riga an kaɗa ƙuri’ar zaɓen sabon jagoran, kuma an cimma matsaya kan wanda zai hau kujerar.
A baya dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da yunƙurin naɗin sabon jagoran, domin ko a jiya Lahadi sai da ya sake jaddada cewa sai ya sa baki a lamarin naɗin sabon shugaban.
A yayin zantawarsa da kafar Talabijin ta ABC gabanin sanar da naɗin na Mojtaba, Trump ya kuma yi barazanar cewar duk wani wanda aka naɗa da basu amince da shi ba, to ko shakka babu za su kauda shi, kamar yadda itama rundunar sojin Isra’ila ta yi irin wannan barazana.
To sai dai Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi, ya ce Tehran ce ta zaɓi sabon jagoran ba tare da katsalandan daga wani ko wata ƙasa ba.
Ana dai yi wa sabon jagoran kallon mai ra’ayin ’yan mazan jiya, musamman saboda alaƙarsa da dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran.
Wane ne Mojtaba Khamenei?
Bayan zama tsakanin jiga-jigai a fannin addini da na siyasa da dukkanin ɓangarorin tafiyarwa na Iran ne, masu ruwa da tsaki na ƙasar suka amince da naɗin Mojtaba Khamnei a matsayin sabon jagoran addini na ƙasar don maye gurbin mahaifinsa da Amurka ta kashe cikin makon jiya.
Mojtaba Khamnei masanin addinin Islama da aka haifa ranar 8 ga watan Oktoban 1969, shekaru kaɗan gabanin kafuwar gwamnatin juyin-juya hali ta Iran, ya taso a gidan malamai kuma yana da ’ya’yan Khamnei mafiya kusanci da shi.

Duk da kasancewarsa ba mai riƙe da wani muƙami ba, amma yana da matuƙar tasiri a tafiyar da gwamnatin ƙasar kasancewarsu babban hadimi kuma mai bayar da shawara ga Ayatollahi Ali Khamnei.
Mojtaba Khamnei mai shekaru 57 haifaffen yankin Mashhad na Iran a shekarar 2004 ne ya auri mai ɗakinsa, Zahra Haddad Adel, inda bayanai ke cewa yana da yara kodayake Mohammad Bagher Khamnei aka fi sani a cikin yaran.
Mojtaba na da alaƙa mai kyau da dakarun juyin-juya hali na Iran, kuma an ga yadda ya gwabza a yaƙin da ƙasar ta yi da Iraqi a shekarun 1980 zuwa 1988 lokacin yana matashi.
Tun kafin rasuwar mahaifinsa, Mojtaba Khamnei ana masa kallon wanda zai iya riƙe kujerar ta jagoran addini saboda ra’ayinsa na ƴan mazan jiya da kuma yadda ya ke bin sahun mahaifinnasa a batutuwa da dama.
Wasu majiyoyi na cewa, Mojtaba shi ke da wuƙa da nama a fagen zartas da batutuwa da dama da mahaifinsa ke aiwatarwa.
Tuni dai ya samu mubaya’a daga ilahirin mambobin majalisar ƙolin addinin Musulunci ta Iran, haka zalika dukkanin ɓangarorin siyasa dama ɗaiɗaikun jama’ar ƙasar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link