Majalisar Dattawa Za Ta Gayyaci Kyari Kan Zargin Giɓin Kuɗi Har Naira Tiriliyan 210 A NNPCL
[ad_1]
Majalisar Dattawan Nijeriya ta jaddada cewa tsohon Babban Darakta na rukunin kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Mele Kyari, tare da wasu tsofaffin manyan jami’an kamfanin mai na ƙasa dole su yi bayani kan giɓin kuɗi da ya kai kusan naira tiriliyan 210 da aka gano a cikin rahotannin binciken kuɗaɗen kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a, Aliyu Wadada, ya ce za a gayyaci tsoffin shugabannin kamfanin domin su bayyana a gaban kwamitin a wani zaman sauraro na jama’a domin su yi karin haske kan batutuwan da aka bankaɗo a rahotannin binciken kuɗin.
- Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 8.4 Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro A Abuja
- Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Wasu Masallata A Zamfara
Wadada ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya jaddada cewa kwamitin ya kuduri aniyar gano gaskiyar abin da ya haifar da wannan giɓin kuɗin.
A cewarsa: “Za mu gayyace su su bayyana a gaban kwamitin a zaman sauraro na jama’a domin su fayyace gaskiyar batu kan wannan lamari mai cike da cece-kuce, ruɗani kuma wanda ba za a amince da shi ba.
“Ana kammala bukukuwan Sallah, za mu rubuta musu takardar gayyata ta hannun Babban Manajan Darakta (GMD) na NNPCL,” in ji shi.
[ad_2]
Source link