Ko Shirin Ciyar Da Mabuƙata Buɗa Baki Na Bilyan Ɗaya Ya Yi Tasiri A Sakkwato?


Watan azumi muhimmin lokaci ne da mabuƙata ke buƙatar sanyayawa daga gwamnatoci, ‘yan uwa da masu hannu da shuni domin gudanar da ibada a cikin sauƙi musamman domin rage masu raɗaɗin matsin tattalin arziki.

A Sakkwato akwai ɗimbin al’ummar da suka dogara da ciyarwar buɗa baki da mabambantan gwamnatoci a jihar ke yi a tsayin shekaru domin sa wa a baka kasancewar ba su da zarafin ciyar da kan su a watan mai albarka.

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 19
  • Harin Iran: Amurka Da Isra’ila Sun Bata Lissafi

A yayin da watan Ramadan ya shiga mako na biyu labari ya yaɗu a kafafen sadarwar zamani cewar wata sabuwa ta bayyana a Sakkwato a yayin da gwamnatin jihar ke raba garin kwaki da ƙuli- ƙuli a matsayin abincin buɗa baki.

Lamarin ya ɗauki hankalin al’umma musamman ganin irin maƙuddan kuɗin da gwamnatin jihar ta ware kan ciyarwar amma kuma a rabawa mabuƙata gari a watan Ramadan.

Shin da gaske gwamnatin jihar ta raba garin kwaki da ƙuli- ƙuli? Idan ta raba a waɗanne cibiyoyin buɗa baki ne aka yi rabon ko kuwa a duka cibiyoyin buɗa bakin ne aka raba garin?

LEADERSHIP Hausa ta kasa gano wata unguwa ko wani gari da aka ga gwamnatin jihar ta raba garin kwaki da ƙuli- ƙuli a matsayin abincin buɗa baki kamar yadda aka labarta labarin a soshiyal midiya, haka ma babu rahoto kan wani ɗan siyasa ko masu hannu da shunin da suka raba garin kwaki da ƙuli- ƙuli a faɗin jihar a watan Ramadan.

Hasalima ofishin Kwamishinan Addinin Musulunci na jihar, Dakta Jabir Sani Mai- hula ya wallafa sanarwa a shafinsa na Facebook inda ya bayyana cewar ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a zancen raba gari da ƙuli- ƙuli ga al’umma a yayin buɗa baki.

Ma’aikatar ta bayyana cewar suna raba abinci mai kyau ga al’ummar jihar wanda kuma ma’aikatar ke sa idanu da ziyarar gani da ido ga cibiyoyin buɗa bakin domin tabbatar da bin ƙa’idojin shirin ciyarwar yadda ya kamata.

Rahotanni a jihar sun tabbatar da cewar kamar yadda ta saba a kowace shekara, gwamnatin jihar Sakkwato a azumin bana ta jagoranci gudanar da shirin ciyar da al’ummar jihar buɗa baki da manufar raba kwanan abinci 34, 000 a kullum.

A yayin da wasu gwamnatocin jihohi ke ware ɗaruruwan miliyoyi domin shirin buɗa bakin Ramadan na shekarar 2026, Gwamnatin jihar Sakkwato ta keɓe tsabar kuɗi har naira bilyan ɗaya musamman domin amfanin al’umma dubu 986, 000.

A yayin ƙaddamar da shirin ciyarwar, Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewar ciyar da mabuƙata a lokacin Ramadan na ɗaya daga cikin ƙudurorin gwamnnatin sa na sanyawawa jama’a a lokacin buƙata.

A shirin na bana gwamnatin jiha ta ƙara adadin cibiyoyin buɗa baki daga 155 zuwa 170 a bisa ga ƙorafe- ƙorafen buƙatar ƙarin cibiyoyin ta yadda kowace cibiya za ta riƙa kula da buɗa bakin aƙalla mutane 200 a lokaci ɗaya.

Kuɗin shirin biliyan ɗaya kamar yadda Gwamnatin ta bayyana sun ƙunshi sayen kayan abinci, biyan ma’aikata da sauran kuɗaɗen gudanarwa domin tabbatar da aiwatar da shirin cikin tsari da nasara.

Kwamitin shirin ciyar da mabuƙata buɗa baki na gwamnatin Sakkwato yana a ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Galadiman Garin Sakkwato, Alhaji Aliyu Attahiru Galadanchi a yayin da Ma’aikatar Lamurran Addini a ƙarƙashin jagorancin Dakta Jabir Mai-hula ke sanya idanu.

Gabanin lokacin shan ruwa, ƴan kwamitin shirin kan fara shirye-shiryen da suka haɗa da tsara kayan abinci, rabawa da kuma tabbatar da cewa komai ya kammala cikin tsafta da nagarta. A na shirya abincin cikin kulawa domin tabbatar da cewa ya kai ga duk wanda ya cancanta ba tare da tangarɗa ba.

Haka kuma, ‘yan kwamitin kan tsara layuka cikin tsari tare da sanya ido kan yadda ake rabon domin gujewa cunkoso da wawaso a a yayin da tuni mabuƙata suke hallara a cibiyoyin suna zaman jiran lokacin shan ruwa.

Abincin da kwamitin ke rabawa shine, shinkafa da miya da naman kaji, kunu, ƙosai, alale, lemu, dabino da ruwa ga ɗimbin mabuƙatan da ke ke buɗa baki a cibiyoyin a kowace rana

Gwamna Ahmed Aliyu a yayin ƙaddamar da shirin ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin shirin tallafin jinƙai da nufin rage raɗaɗin azumi ga al’ummar Musulmi tare da ƙarfafa tausayi, haɗin kai da goyon bayan juna a cikin watan Ramadan mai alfarma.

“Ina ba ku tabbacin cewa abincin zai kasance mai tsafta, an shirya shi cikin tsari mai kyau kuma mai inganci. Haka kuma, an ɗauki ma’aikatan wucin gadi domin tabbatar da tafiyar da shirin cikin nasara a duk tsawon watan Ramadan.” In ji Gwamnan a yayin ƙaddamar da shirin.

Ya ce shirin rabon abincin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na bunƙasa fa’idojin Musulunci da walwalar al’umma. Ya ce hakan ya haɗa da gyaran masallatai da makarantu tare da biyan alawus na wata-wata ga masallatan Juma’a domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamnan ya ce shirin wanda aka ƙaddamar shekaru 19 da suka gabata a zamanin mulkin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, ya ci- gaba da samar da sauƙi da tallafi ga dubban al’ummar jihar, lamarin da ke nuna jajircewar jihar wajen yaƙi da talauci da inganta rayuwar al’umma.

Shin kwamitin buɗa bakin na gudanar da aikin ciyarwar yadda ya kamata, ko gwamnatin jihar ta gamsu da yadda buɗa bakin ke tafiya kuma yaya take gani da kallon alfanu ko tasirin shirin?

Da yake bayyana ra’ayinsa kan shirin ciyarwar, tuni Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya bayyana gamsuwa da inganci da wadatar abincin buɗa baki da gwamnatin ke aiwatarwa a watan Ramadan a ƙarƙashin shirin ciyarwa na naira bilyan ɗaya.

Aliyu ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci cibiyoyin buɗa bakin azumi da ke kan titin Clapperton, Lodge Road, Gidan Dallatu, Asibitin Ƙwararru da kuma yankin Maɗunka a inda ya gana da masu cin gajiyar shirin tare da mambobin kwamitocin ciyarwar.

Da yake jawabi bayan kammala duba cibiyoyin, Gwamnan ya yabawa kwamitin ciyarwar yana mai cewa an samu gagarumin ci- gaba a yadda ake gudanar da shirin idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ya ce ya gamsu da abin da ya gani a cibiyoyin a kan hakan ya buƙaci mambobin kwamitocin cibiyoyin ciyarwar da su ci- gaba da ƙara ƙaimi da jajircewa wajen tabbatar da cikar manufofin shirin.

“Manufar wannan shiri ita ce tallafawa marasa galihu ta hanyar samar musu wurin buɗa baki cikin sauƙi, saboda haka muna buƙatar ƙarin jajircewa daga kwamitocin cibiyoyin ciyarwar.” In ji gwamnan.

Haka kuma, ya yi kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su taimaka wajen marawa ƙoƙarin gwamnati baya ta hanyar kafa cibiyoyin ciyarwa a cikin al’ummominsu don tallafawa marasa galihu.

Malam Harande Sani, mazaunin Unguwar Rogo, ya bayyana shirin a matsayin abin a yaba, yana mai cewa yana taimakawa marasa galihu musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa. “Wannan shiri ya rage mana nauyi sosai a watan Ramadan. Mutane da dama da ba su da hali ire- ire na suna samun damar buɗa baki cikin kwanciyar hankali.”

A nasa ɓangaren Kallamu Gandi daga unguwar Bado cewa ya yi “Shirin yana da muhimmanci matuƙa domin yana tallafawa dubban iyalai. Ina ganin gwamnati ta yi ƙoƙari amma ya kamata a ƙara yawan abinci ko cibiyoyi domin rage cincirindon jama’a da ke akwai a wasu cibiyoyin.”



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *