Tsohon Kwamishinan kuɗi na Kano, Farfesa Kabiru Dandago, ya rasu
Farfesa Kabiru Isa Dandago, Tsohon Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano a zamanin Gwamna Abdullahi Ganduje, ya rasu.
Ya rasu ne da yammacin ranar Laraba a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano.
Daraktan Yaɗa Labarai na Jami’ar Bayero, Lamara Garba, ya tabbatar da rasuwar Farfesan.
Farfesa Dandago ya koyar da lissafin kuɗi da haraji a Tsangayar Ilimin Zamantakewa da Gudanarwa.
Garba, ya rubuta cewa, “Cikin alhini nake sanar da rasuwar Farfesa Dandago. Kwanan nan ya ba da gudummawa a asusun tallafa wa iyalan abokan aikinmu da suka rasu.
“Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya shi a Jannatul Firdausi. Amin.”
A makon da ya gabata, Cibiyar Nazarin Musulunci ta Duniya (IIIT) ta gayyace shi domin halartar laccar Ramadan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za a tattauna da su.
Farfesa Dandago ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Kuɗi daga watan Yunin 2015 zuwa Oktoban 2018 a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.
Ya fara aiki a Jami’ar Bayero a watan Satumban 1990, kuma daga baya ya zama Shugaban Tsangayar Ilimin Zamantakewa da Gudanarwa.
A tsawon lokacin aikinsa, ya rubuta tare da gyara littattafai da dama kan nazarin kuɗi, haraji, kuɗi da tattalin arziƙi.