AFC ta ɗage wasanni saboda yamutsin da ya mamaye Gabas ta Tsakiya
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Asia (AFC) ta sanar da ɗage dukkan wasanni da aka tsara yi ƙarkashin gasar cin kofin nahiyar da Champion’s Ligue a ranakun 2 zuwa 3 ga wannan.
AFC ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon yamutsin da ya mamaye Gabas ta Tsakiya biyo bayan hare-haren haɗin gwiwar da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran.
Kamar dai yadda hukumar mai mazauni a Kuala Lumpur babban birnin Srilanka ta sanar, wasannin da lamarin ya shafa sun haɗa da wanda za a buga tsakanin ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiya da Al-Duhail ta Qatar.
Sauran wasannin da aka ɗage sun hada da wanda za’a kara tsakanin club ɗin Shabab Al-Ahli ta Dubai da Tractor ta Iran sai kuma wasan da zai hada ƙungiyar Al-Wahda ta Hadaddiyar Daular Laraba da takwararta ta Al-Ittihad.
Tuni dai hukumar ƙwallon kafar Iran ta ce tana nazarin ƙauracewa shiga Gasar Kofin Duniya ta shekara 2026 da Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci, yayin da rage watanni huɗu da soma gasar.
Kazalika, magatakarda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA ), Mattias Grastrom ya ce suna bibiyar sau da ƙafa abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.
Wannan dai na zuwa yayin da wata tawagar FIFA ke shirin isa Mexico domin duba halin da aka shiga sakamakon tarzoma da ta ɓarke biyo bayan kisan gagarumin ɗan safarar miyagun ƙwayoyin nan El-Mancho da dakarun ƙasar su ka yi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link