Girke-girken Azumi (2)
[ad_1]
… ci gaba daga makon da ya gabata.
Daga nan sai kayan soye-soye da dan dahuwar nama ki kayata dahuwar namanki ta yi kyau da dadi ya yi dan room-romo yadda ana ci ana shan romon wani kuma yana bukatar romon ya zuba a soyayyan dankali ko doya shi ya sa ake so ya yi yawa romon.
Sahur:
Ya kamata uwargida ki san abincin da maigida ya kama ta ko yake so ya ci lokacin, wani yana so ya ci tuwo a sahur wani kuma kunu wani kuma shayi wani kuma ko me ya samu ba shi da zaBi, to duk koma mene ne ki yi kokarin tanadar sa kafin sahur din, ana so a samu abinci mai dan nauyi-nauyi saboda ya rike ciki kar a ji yunwa da wuri kamar tuwo, shinkafa da dai sauransu.
Ya kamata uwargida ki dan hada lemon, ki sa shi ya dan yi sanyi-sanyi saboda bayan an gama cin abinci ana dan korawa, ba wai sai zoBo ba kullum ba yau idan kika yi wancan gobe wancan haka za ki rika yi.
Yadda Za Ki Hada Lemon Kankana Da Situro Beri:
Abubuwan da ake bukata:
Kankana, Siruro beri, Madara amma Fresh Milk, balilla, Ice- cream, Wufcream:
Za ki samu Kankanarki daidai yadda kike son yawansa sai ki wanke ta ki cire bayan sannan ki yayyanka ta kamar yankan sha, sai ki wanke Sitiru berin ki rarraba shi gida biyu a tsaye haka, sai ki nika su tare da Sitiru berin amma kar ki zuba shi duka za ki rage wanda za ki jera a sama, sannan ki kawo ice-ceam ki zuba shi sai fresh milk din ita ma ki zuba ta amma ita ana so a zuba ta da dan yawa, sai ki markada, idan ya markadu sai ki bude shi ki zuba balillar kamar babban cokali daya saboda ya dan yi kamshi, ki juya shi ki zuba a kofi ki sa a Firij ya yi sanyi.
Hadin lemon cafman koktail: (Chapman Cocktail) A turance hadin Nijeriya:
Abubuwan da za a tanada:
Fanta, Sifirayit, Sumob, Girenadil shiruf, Sitoru beri, Lemon tsami, Layin, Rabina, Kokumba,
Yadda ake hadawa:
Da farko za ki hada Fanta da Sifirayit da Somub da Rabina a waje daya, sannan ki yanka Kokumba ki ajiye ta a gefe, sai Sitoru beri shima ki yanka shi ki ajiye shi a gefe, sai Lemon tsami shima ki yanka shi Cicle sai layim shima ‘Cicle’ sai ki dakko wancan Lemon da kika hada su waje daya ki zuba su a cikin juice dispenser sai ki dakko wadannan abubuwan da kika yayyaka su sai ki zuba a ciki sai ki dan disa girenadin shiruf dinki a ciki idan kina bukata shi ba dole bane yana kara kamshi da dadi sai ki gauraya su shiken ki rufe, komai ya kammala.
[ad_2]
Source link