Za mu kai wa Amurka da Isra’ila harin da ba su taɓa gani ba — Iran

[ad_1]



Babban jami’in tsaron ƙasar Iran ya gargaɗi Amurka da Isra’ila cewa za su kai musu hari mai tsanani irin wanda ba su taɓa fuskanta ba a baya.

Wannan gargaɗin na ƙunshe ne cikin wani saƙo da Ali Larijiani ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadin nan.

“Jiya (Asabar) Iran ta harba makamai masu linzami kan Amurka da Isra’ila, kuma harin ya yi tasiri sosai. Amma yau za mu kai musu hari da wani irin ƙarfi da ba su taɓa gani ba.”

Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran barazanar kai mata harin da duniya ba ta taɓa ganin makamancinsa ba.

“Iran ta bayyana cewa za ta kai hari mana tsanani fiye da duk wanda aka taɓa kai wa a baya,” in ji Trump a shafukan sada zumunta.

“Bai kamata su yi hakan ba, domin idan suka yi, za mu kai musu hari da wani ƙarfi da duniya ba ta taɓa gani ba.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa a watan Agustan bara ne aka naɗa Ali Larijani a matsayin Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran (SNSC).

Tun daga wancan lokaci, ya riƙe manyan muƙamai tun bayan da ta bayyana a matsayin mai cikakkiyar biyayya ga Jagoran Addini Ali Khamenei.

Haka kuma, ya shahara wajen ƙulla mu’amala mai hikima da ɓangarori daban-daban na tsarin siyasar ƙasashen da ke yawan saɓani a tsakaninsu.

Matsayinsa ba amintaccen ga Khamenei ya ƙara bayyana a watan da ya gabata, lokacin da ya kai ziyara ƙasar Oman a matsayin mai shiga tsakani, domin share fagen tattaunawar nukiliya ta kai-tsaye da Amurka.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da Washington ke ƙara jibge dakarunta a yankin Gabas ta Tsakiya, a ƙoƙarin matsa wa Iran lamba ta amince da wasu buƙatu gabanin hare-haren da suka biyo baya.

Haka kuma, Larijani ya kai ziyara sau da dama zuwa Moscow, babbar ƙasar ƙawancen Iran, a ‘yan watannin nan, inda ya tattauna batutuwan tsaro daban-daban.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *