‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga A Wani Yunƙurin Sace Mutane A Abuja

[ad_1]


Rundunar ‘Yansanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, ta daƙile wani yunƙurin sace mutane a ƙauyen Guto, da ke bayan gari a Yankin Bwari.

Lamarin, wanda ya faru da sanyin safiyar Alhamis, an yi nasara kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar yayin da wani jami’in ‘yansanda ya rasa ransa a yayin bata kashin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan FCT, SP Josephine Adeh, a cikin wata sanarwa, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:10 na tsakar dare, lokacin da rundunar ta sami kiran gaggawa game da masu kai hari kusan 30 ɗauke da makamai waɗanda suka mamaye al’umma, da nufin sace wani mutum da iyalansa.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘Yansandan FCT, CP Miller Dantawaye, wanda ya ziyarci yankin, ya tura ƙarin jami’ai zuwa al’ummar da aka kai wa harin don tsaurara tsaro.

Dantawaye ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike don tabbatar da cewa, an kama waɗanda suka tsere da raunin harbin bindiga zuwa daji.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *