Sin Na Taka Rawar Gani A Fannin Saukaka Tsadar Lantarki A Duniya

[ad_1]


Tuni kasar Sin ta yi nasarar kafa managarcin tsarin samarwa da cinikayyar lantarki daga hanyoyi mabanbanta. Kasar Sin ta wuce gaba a matsayin jagora a fannin samar da lantarki daga hasken rana, da karfin iska, da ma fasahohin da ake amfani da su a ababen hawa masu aiki da lantarki da ma adana lantarkin, wanda hakan ya sanya ta zama jigo a fannin sauyi zuwa amfani da makamashi marar gurbata yanayi.

Wasu alkaluma da hukumar kasa da kasa mai lura da makamashi da ake iya sabuntawa ta fitar a baya bayan nan, sun nun yadda aka samu raguwar tsadar makamashin lantarki a duniya baki daya, musamman wanda ake samarwa daga hasken rana da iska, lamarin da ake alakantawa da babbar gudunmawar kasar Sin.

Bisa manufofinta, Sin ta yi matukar kokari wajen saukaka farashin makamashi mai tsafta ga dukkanin sassan duniya. Daya daga cikin misalai kan hakan shi ne shirin “Zirin lantarki ta hasken rana na Afirka”, wato muhimmiyar manufar hadin gwiwa ta kasashe masu tasowa dake da nufin shawo kan sauyin yanayi, wadda aka kaddamar a shekarar 2023.

Karkashin shirin, Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da kasashe irinsu Burundi da Chadi a nahiyar Afirka, domin hade fifikon masana’antunta da yalwar hasken rana na sassan Afirka, ta yadda hakan zai taimakawa al’ummun nahiyar Afirka samun lantarki mai dorewa.

Tuni wannan hadin gwiwa tsakanin kamfanonin Sin da na kasashen Afirka, ya samar da lantarki ta hasken rana da ya zarce jimillar gigawatts 1.5.

A daya bangaren kuma, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen ingiza manufar rage fitar da hayakin carbon mai dumama yanayi tsakanin kasashen duniya.

Ana iya ganin wannan kwazo na kasar Sin daga yadda a shekarar 2024 kadai, ta fitar da tarin kayayyaki masu kunshe da fasahohin makamashi mai tsafta, wadanda aka tabbatar sun taimaka wajen rage fitar da hayakin cabon a wajen kasar, da kaso daya bisa dari cikin na jimillar kasashen duniya.

Masharhanta dai na ganin domin cimma burin da ake fata, kamata ya yi sassan kasa da kasa su kara fadada cudanya da juna, a fannin sauya akala zuwa nau’o’in makamashi marasa dumama yanayi, su yaukaka musayar fasahohi da tsare-tsare a fannin, tare da karfafa matakan cin gajiyar fasahohin kasar Sin na samarwa, da amfana daga makamashi mai tsafta, ta yadda hakan zai amfani daukacin sassan duniya baki daya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *