’Yan sanda sun bindige Lakurawa 3 har lahira a Kebbi
[ad_1]
’Yan sanda sun harbe wasu mayaƙan Lakurawa har lahira a yayin da ragowar suka tsere a yankin Gorun Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Dandi da ke Jihar Kebbi.
Kakakin rundunar, SP Nafi’u Abubakar , a cikin wata sanarwa a ranar Asabar ya ce bayan samun rahoton harin ’yan ta’addan a yankin ne ’yan sanda suka je suka yi musayar wuta na tsawon awannin da su, inda suka halaka mutum 3 a cikin maharan, ragowar kuma suka cika bujensu da iska.
Sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ta ce bayan samun rahoto ne DPO na yankin Lamba ya tura ’yan sanda da ’yan banga domin fatattakar maharan,
Ya ce an ƙwace babur guda ɗaya da mayaƙan na Lakurawa suka tsere suka bari.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar Bello M. Sani ya jinjina wa DPOn da dakarunsa bisa ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Ya ƙara da kira a gare su da su ƙara zage dantse domin fatattakar Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da masu laifi a jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link