Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
[ad_1]
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tuna yadda ya sayar da kadarorinsa don ɗaukar nauyin matasa maza da mata 370 daga jihar Kano don yin karatu a kasashen waje.
A yayin da wadanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na Kwankwasiyya suka gudanar da taron su na shekara-shekara don godiya ga wannan tallafin, Kwankwaso ya bayyana ilimi a matsayin gado mafi dorewa da kowane shugaba zai iya gadar wa al’umma.
- Mutum Biyu Sun Rasu Yayin Rikici Tsakanin Jami’an Tsaro Da Matasa A Katsina
- Sin Za Ta Aiwatar Da Manufar Harkokin Kudi Mai Inganci A 2026
Da yake jawabi a wurin taron mai tarihi, Jagoran ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya nuna masa irin wannan “rana mai tarihi ga jihar Kano da Nijeriya,” yana mai lura da cewa taron ya hada jigogi a fannin ilimin zamani da aka dauki nauyinsu tsawon kusan shekaru 25.
“Ina tuna yawancinku a baya. Wasu daga cikinku sun yi kama da wadanda suka fito kai tsaye daga kauyuka. A yau, ina ganin kwarin gwiwa, kwarewa har ma wasunku sun manyanta, har da furfura a kansu” in ji shi
A cewar wata sanarwa da Dakta Mansur Hassan ya fitar, Kwankwaso, wanda ya mulki jihar Kano tsawon shekaru takwas, ya ce taron ya jaddada muhimmancin shugabanci, dorewa da kuma saka hannun jari na dogon lokaci a fannin rayuwar dan adam.
Ya bayyana cewa bayan babban zaben 2019, lokacin da gwamnati ta dakatar da daukar nauyin daliban kasashen waje, shi da kansa ya ci gaba da wannan shiri ta hanyar Gidauniyar Ci Gaban Kwankwasiyya (KDF).
Kwankwaso ya kara da cewa, bayan malaman da gidauniyar ta dauki nauyinsu, shirin ya ci gaba da tallafa wa dalibai sama da 3,000 cikin shekaru hudu don yin karatu a kasashe 14 a Turai, Asiya, Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Shirin ya samar da likitoci, injiniyoyi, matukan jirgi da kwararru a duniya. Bayanan da ake da su daga KDF, sun nuna cewa shirin ya zuwa yanzu ya samar da daruruwan likitoci da kwararru da ke aiki a asibitocin koyarwa a Nijeriya da kasashen waje; kwararrun matukan jirgi da ma’aikata a filin jiragen sama; dubban injiniyoyi, kwararru a fannin fasahar sadarwa; da kuma malamai da masu bincike, tare da sama da masu digirin digirgir 300 da aka bayyana a taron.
Ta kuma samar da masana magunguna, masu gine-gine, masana tattalin arziki, lauyoyi, kwararru kan manufofin jama’a da masu aikin ci gaba da ke aiki a fadin Nijeriya, Afirka, Turai, Arewacin Amurka da Gabas ta Tsakiya.
Kwankwaso ya bayyana cewa manufar gidauniyar ba wai kawai daukar nauyin malamai ba ne, har ma da jagorantar su, bin diddigin su da kuma hada su cikin ayyukan gwamnati, shugabanci da ci gaban kasa.
[ad_2]
Source link