Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu

[ad_1]



Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci.

A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci.

Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba.

Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da tsadar rayuwa, rashin tsaro, da rashin shugabanci na gari, kuma wannan hukunci na iya ƙara tayar da hankali.

“Ƙorafe-ƙorafen da Kanu ya yi ba sabbi ba ne. Suna buƙata hikima, tausayi da sauraro. A wasu ƙasashen, irin waɗannan koke-koke ana magance su ta hanyar tattaunawa da gyare-gyare domin ƙarfafa haɗin kai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama suna amfani da hanyar siyasa ko sulhu idan hukuncin kotu kaɗai ba zai kawo zaman lafiya ba.

“Wannan abun takaici na iya ƙara tsananta rashin tsaro. Kama shi, tsare shi da hukunta shi alama ce ta gazawar jagoranci da rashin fahimtar matsalar tun da farko,” in ji Obi.

Obi ya yi kira ga gwamnati, dattawa, da shugabannin ƙasa su yi aiki don nemo mafita game da zaman lafiya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *