Tsaro: Gwamnatin Kogi ta rufe kasuwanni da tashoshin mota a ƙananan hukumomi 7

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kogi, ta rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota a ƙananan hukumomi bakwai da ke yankin yammacin jihar, domin inganta matakan tsaro.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar kamo ’yan ta’adda, ’yan fashi da sauran masu aikata laifuka suka ɓuya a wasu sassan jihar.

Fanwo, ya ce rufe kasuwannin da tashoshin mota na wucin gadi zai daƙe ’yan ta’adda da masu ba su bayanai.

Ya bayyana cewa matakin ya shafi ƙananan hukumomin Lokoja, Kogi, Kabba/Bunu, Ijumu, Mopa Muro, Yagba ta Yamma da Yagba da Gabas.

A cewarsa, rufewar ɗan wani lokaci ce, kuma za a buɗe wuraren nan take bayan kammala ayyukan tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa ana gudanar da aikin tsaron ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro da kuma shugabannin hukumomin tsaro a Jihar Kogi.

Har ila yau, ya ce gwamnatin jihar ta rufe dukkanin makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *