An Yi Biki Mai Jigon “Barka Da Sabuwar Shekarar Sinawa” A Najeriya
[ad_1]
A ranar 7 ga Fabrairu, an gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa mai jigon “Barka da Sabuwar Shekarar Sinawa” na Najeriya na shekarar 2026 da kuma bikin al’adu na murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya cikin nasara, a cibiyar yada al’adun Sin dake Abuja, wanda ofishin jakadancin Sin dake Najeriya da kungiyar musayar al’adu da kasashen waje ta Sin da sauran hukumomi suka dauki nauyin shiryawa tare da hadin gwiwar babbar hukumar kula da kasuwanci ta Sin dake Najeriya.
Zhou Hongyou, mai taimakawa na musamman ga jakadan Sin a Najeriya, ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa shekarar 2026 ita ce shekarar Doki ta Sinawa, ita ce kuma ta cika shekaru 55 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, da kuma “Shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka”. Kasar Sin tana son yin aiki da Najeriya don gina al’umma mai makoma ta bai-daya a matakin koli, da ci gaba da karfafa amincewa da juna a siyasance da goyon bayan juna, da zurfafa hadin gwiwa mai amfani, da inganta mu’amala da hadin gwiwa a fannin al’adu, da kuma tabbatar da cewa abotar dake tsakanin Sin da Najeriya za ta samu karbuwa daga zuriya zuwa zuriya, kana da yadda sakamakon hadin gwiwarsu zai amfanar da al’ummun kasashen biyu.
Joseph Tegbe, babban darakta mai kula da dangantakar abokantaka tsakanin Najeriya da Sin bisa manyan tsare-tsare, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga al’ummar Sin a madadin shugaban Najeriya Bola Tinubu, kuma ya sake nanata goyon bayan Najeriya ga manufar Sin daya tak a duniya.
Ya bayyana cewa Najeriya tana son yin aiki tare da Sin don ci gaba da aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a lokacin ziyarar aiki ta shugaba Tinubu a Sin a watan Satumba na shekarar 2024, da kuma bunkasa dangantakar abota tsakanin Najeriya da Sin bisa manyan tsare-tsare zuwa hadin gwiwa mai zurfi da samun kyakkyawar makoma ta bai-daya.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link