Tinubu ya naɗa Taiwo Oyedele Ministan Kuɗi
[ad_1]
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Taiwo Oyedele a matsayin Ƙaramin Ministan Kuɗi, inda ya maye gurbin Doris Uzoka-Anite.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar wannan Talatar.
Sanarwar ta ce Uzoka-Anite za ta koma Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Ƙasa a matsayin Ƙaramar Minista, wanda shi ne sauyin muƙami na uku a da aka yi mata a wannan gwamnati.
Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio sunan Oyedele domin tantancewa.
Kafin naɗin nasa, Oyedele, wanda ɗan asali garin Ikaram ne na Ƙaramar Hukumar Akoko ta Jihar Ondo, shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Gyara Tsarin Haraji, wanda ya jagoranci sauye-sauyen haraji a ƙasar.
Oyedele, mai shekaru 50, masani ne a fannin tattalin arziki da lissafin kuɗi.
Ya yi karatu a Kwalejin Fasaha ta Yaba (YABATECH), sannan ya samu digiri a Oxford Brookes University.
Haka kuma yi wasu kwasa-kwasai na ƙarin ilimi a Makarantar Tsimi da Tattalin Kuɗi da ke Landan, da Jami’ar Yale, da Harvard Kennedy da ke Amurka.
Ya shafe shekaru 22 yana aiki a kamfanin PwC, inda ya kai matsayin abokin hulɗa kan manufofin haraji a Afirka.
Haka kuma farfesa ne a Jami’ar Babcock da kuma baƙuntar malanta a Makarantar Nazarin Kasuwanci da ke Legas.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link