Tinubu Da Shettima Sun Yi Buɗa-Baki Da Sarakuna Da Malaman Addini A Villa

[ad_1]

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da Mataimakinsa Kashim Shettima sun yi buɗa-bakin azumin watan Ramadan tare da sarakuna da kuma shugabannin addinai a Banquet Hall na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Villa, Abuja.

Taron buɗa-bakin wanda ya gudana a ranar Litinin ya haɗa manyan shugabannin gargajiya da malaman addini daga sassa daban-daban na ƙasar, inda suka taru domin yin addu’o’i da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.

Wannan taro na daga cikin al’adun da fadar shugaban ƙasa ke yi a watan Ramadan, inda ake haɗa shugabanni da masu ruwa da tsaki domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *