Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 3, sun ƙwato makamai a dajin Sakkwato

[ad_1]



Dakarun Sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma, sun kashe wasu ‘yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai yayin wani samame a dajin Kadam da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Ya ce dakarun wata bataliya ta musamman ce suka gudanar da farmakin bayan samun bayanan sirri kan matsugunnin ‘yan ta’addan.

Olaniyi ya ce bayanan sirrin sun nuna cewa sama da ‘yan ta’adda 100 sun taru a cikin dajin domin shirya hare-hare da sace mutane a garuruwan da ke kewaye, lamarin da ya sa dakarun suka kai musu farmaki inda aka gwabza faɗa mai zafi.

A cewarsa, bayan artabun, an kashe ‘yan ta’adda uku yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi, yayin da sojojin suka ƙwato bindigar PKT, bindigogi AK-47 guda biyu, harsasai, rediyoyin sadarwa, babura uku da wayar hannu, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da sintiri domin kamo sauran ‘yan ta’addan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *