Sinner zai gwabza da Djokovic a wasan daf da ƙarshe
[ad_1]
A gasar Tennis ta Australian Open da ake yi a Melbourne, Jannik Sinner ya kai wasan daf da ƙarshe.
Zakaran da ke kare kambunsa mai fatan lashe na uku a jere ya do ke Ben Shelton da cin 6 – 3, 6-4, 6-4, kuma yanzu zai fafata da Novak Djokovic.
Shima Djokovic ya tsallaka karawar daf da ƙarshe bayan abokin wasansa Lorenzo Musetti ya janye sakamakon rauni. Musetti yana cin ɗan kasar Serbia, kafin ya ji raunin.
A ɓangaren mata kuwa, Elena Rybakina ta kai daf da ƙarshe, bayan da ta doke Iga Swiatek da cin 7-5, 6-1.
Ita kuwa Rybakina za ta fafata da Jessica Pegula, wadda ta ta yi waje da Amanda Anisimova da cin 6-2, 7-6.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link