Ribadu Ya Gana Da Sakataren Yaƙin Amurka Kan Iƙirarin Kashe Kiristoci A Nijeriya

[ad_1]


Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta jaddada damuwarta kan ƙarin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa ɓangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki “da gaggawa” da Nijeriya don rage hare-haren ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da ƙungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a ƙauyuka, da coci-coci da gonaki. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun ruwaito ƙaruwar kashe-kashe, inda alƙalumman baya-bayan nan ke nuna cewa sama da Kiristoci 7,000 aka kashe cikin watanni bakwai na 2025.

Taron ya biyo bayan sace ɗalibai 215 da malamai 12 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja, wanda ya ƙara tayar da hankalin jama’a kan taɓarɓarewar tsaro. Wannan lamari ya kuma ƙara sa Amurka cikin damuwa kan ƙaruwar ayyukan sace mutane da kashe-kashe a karkara.

Shugaba Donald Trump ya sha gargadin Nijeriya game da wannan tashin hankali, yana nuni da yiwuwar tsoma hannu ta hanyar amfani da Sojojin Amurka idan gwamnati ta kasa daƙile ƙungiyoyin da ke haddasa hare-haren. Har ma ta sanya da Nijeriya cikin jerin “ƙasashen da ke da babbar matsala kan ƴancin addini”.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *