Dole Mu Goyi Bayan Kafa Hukumar Samar Da Madarar Shanu – Jega
[ad_1]
Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan bunkasa fannin kiwon dabbobi da kuma sanya ido kan samar da sauye-sauye a fannin, Farfesa Attahiru Jefa, ya bayyana cewa; akwai matukar bukatar a kara karfafa bangaren samar da wadatacciyar madarar shanu a fadin wannan kasa.
Jega, wanda ya kasance daya daga cikin shugabannin kwamitin fadar shugaban kasa na wanzar da sauye-sauye a fannin, ya yi nuni da cewa; ta wannan hanya ce za a iya samun nasarar kara habaka samar da wadatacciyar madarar a wannan kasa.
Farfesan ya bayyana hakan ne a Abuja, a wani taron bita na wanzar da tsarin kasa na samar da madarar shanu, inda ya yi nuni da cewa; fannin ba wai kawai ya dogara ne kacokan a kan samar da madarar ba, har ma da inganta rayuwar jama’a da kuma samar da abinci mai gina jiki tare kuma da samar da damar yin sana’a ga wadanda suka rungumi fannin.
Jega, wanda Farfesa Demo Kalla, Darakta a cibiyar gudanar da bincike da bunkasa samar da madarar da ke Jami’ar Jihar Bauchi, ATBU ya wakilce shi a wajen taron ya kara da cewa; idan aka wanzar da tsarin yadda ya kamata, zai kara karfafa kwarin gwiwar manoma da kuma samar da ayyukan yi ga mata da matasa da suka rungumi fannin na aikin noma.
“Dole ne mu karafafa bayar da goyon bayanmu, domin cimma burin da ake da shi na samar da wadatacciyar madarar shanu a kasar nan,”in ji Jega.
“Ya zama wajibi gwamnatin tarayya, ta samar da kyakkyawan yanayi, su kuma masu zaman kansu su samar da fasahar zamani da zuba hannun jari a fannin, domin kara habaka fannin yadda zai kai mataki irin na duniya,“ a cewar Jega.
“Kamar yadda muka kara karfafa hukumominmu, haka yana da kyau mu samu darasi na kasa da kasa, kamar dai irin na kasashen India, Kenya, Uganda, Rwanda da kuma Ethiopia, musamman kan tallafawar da suke yi wa fannin na samar da madarar shanu.
Farfesa Jega ya kara da cewa, dole ne kasar nan, ta jaddada batun tattaunawa tare da samar da alkaluman rage shigo da madarar shanu daga ketare zuwa cikin kasar nan da kuma samar da kyakkyawan yanayi na yin kasuwanci, musamman domin a rika yin amfani da madarar da ake samarwa a cikin kasar.
[ad_2]
Source link