Nasarar da Arsenal ta samu a gidan Tottenham ta bai wa maraɗa kunya — Gyokeres

[ad_1]



Ɗan wasan gaba na Arsenal, Viktor Gyokeres, ya ce babbar nasarar da ƙungiyarsu ta samu wajen doke abokiyar hamayyarta Tottenham Hotspur ta bai wa masu sukar ƙungiyar kunya.

A Lahadin da ta gabata ce dai Arsenal ta lallasa Tottenham da ci 4–1, lamarin da Gyokere ɗan asalin Sweden ya ce ita ce “amsa mafi dacewa” ga masu sukar ƙungiyar bayan tuntuɓen da Arsenal ɗin ta yi a hanƙoron da take yi na lashe Firimiya Ingila ta bana.

Gyokeres da Eberechi Eze ne suka zura ƙwallaye biyu-biyu a wasan da aka buga a filin Tottenham Hotspur ranar Lahadi, kwanaki huɗu kacal bayan Arsenal ta tashi 2–2 da Wolverhampton Wanderers da ke ƙasan tebur.

Rashin samun nasarar tsira da maki uku da Arsenal ta yi a Molineux ya sake jefa ayar tambayoyi kan kishin ƙungiyar, amma doke Spurs da ta yi ya sanya sun bayar da tazarar maki biyar a saman teburin Firimiyar.

Arsenal, wadda ta tsallake wasannin share fage na Gasar Zakarun Turai ta Champions League, ba za ta buga wasa a tsakiyar mako ba a wannan karon — wanda shi ne karo na farko cikin fiye da watanni biyu da za ta samu sukuni a tsakiyar mako.

Ita ma Manchester City da ke mataki na biyu a teburin Firimiyar ba za ta sake buga wani wasan ba sai karshen mako mai zuwa, inda za ta kara da Leeds United a Elland Road ranar Asabar.

Kocin City Pep Guardiola ya ce zai bar ‘yan wasansa su huta da har su hole a cikin makon, amma kocin Arsenal Mikel Arteta ya mayar da martani cikin murmushi da cewa: “holewa? ba da mu ba ba. Mu dai za mu ci gaba da yin namu shirin.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *