Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba
[ad_1]
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba.
Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya.
A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco.
Za a bayyana gwarazan a rukuni-rukuni daban-daban: maza da mata, masu horarwa, ƙungiyoyi, tawagar ƙasashe, da kuma matasan ‘yan wasa masu tasowa.
Za a fara bikin ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma agogon Morocco da Najeriya, a jami’ar Mohammed VI Polytechnic University (UM6P) da ke Rabat, babban birnin ƙasar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link