Lakurawa sun kashe ’yan canji 2, sun sace miliyoyin kuɗi a Sakkwato
[ad_1]
’Yan ta’addan Lakurawa sun kashe ’yan canji biyu tare da sace kuɗi masu yawa a kasuwar Darusa da ke yankin Kurdula, da ke Ƙaramar Hukumar Gudu ta Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, lokacin da ’yan bindigar suka shiga kasuwar a kan babura huɗu ɗauke da bindigogi.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai wa ’yan canji hari, inda suka kashe Alhaji Ummaru Darusa da Muhammad Sani.
Hakazalika, sun yi awon gaba da kuɗaɗe masu tarin yawa.
Ya ce kasuwar Darusa tana kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, inda ’yan kasuwa daga ƙasashen biyu ke zuwa yin kasuwanci.
Ya ƙara da cewa Muhammad Sani ɗan kasuwa ne daga Jamhuriyar Nijar, da ke yin kasuwanci a kasuwar Darusa.
Mazaunin ya bayyana cewa ana zargin ’yan bindigar sun daɗe suna bibiyar Alhaji Ummaru kafin su samu damar kai masa hari.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara tsaro a yankin.
Lakurawa sun daɗe suna addabar yankunan Gudu da Tangaza, inda suke kai wa ƙauyuka hare-hare.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce harin ya faru ne ranar Alhamis, inda mutum biyu suka rasa rayukansu.
A cewarsa, Alhaji ya rasu a lokacin da aka kai harin, yayin da ɗaya ɗan kasuwar ya rasu a asibitin Dogon Dutse.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link