LABARAN SAFIYAR ALHAMIS 14-08-2025
Labaran Yammacin Laraba 13/08/2025CE – 19/02/1447AH Ga Takaitattun Labaran.
Gwamnatin tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan Comfort Emmanson, fasinjar nan da ake zargi da tayar da hankali a cikin jirgin Ibom Air.
Gwamnatin tarayya ta ce za ta haɗa gwiwa da wasu kamfanoni domin gina titin jirgn ƙasa mai ɗankaren gudu da zai kai tsawon kilomita 4,000 a jihohi shida na ƙasar.
Atiku yace ana amfani da hukumar EFCC ne wajen tursasa wa ƴan adawa komawa APC.
Majalisar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano saboda zargin almundahana.
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa.
Dakarun Sojin Bataliya ta 3 da ke sansanin FOB Rann, a Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, sun daƙile wani hari da ISWAP suka kai.
Hukumar NEMA tace ambaliya ta shafe kadada 350 ta gonaki a Furore ta jihar Adamawa.
Farfesa Gwarzo ya taya wanda ya kafa Jami’ar CEU George Soros murnar cika shekaru 95.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata.
Gwamnatin Neja ta nemi sulhu da gidan rediyon Badeggi FM.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13.
Ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina ta shiga jerin ƙananan hukumomin da suka amince su yi sulhu da ‘yan bindiga, domin kawo ƙarshen tashin hankali a yankin.
Hatsabiban ƴan bindigar da ake nema ruwa a jallo sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Katsina.
Wani ɗalibin ya yi ƙaryar sace shi tare da neman Naira miliyan 50 daga hannun mahaifiyarsa a jihar Neja.
An kama tsohon firaministan Mali kan zargin lalata kayan gwamnati.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Amurka “za ta ci gaba da goyon bayan Ukraine.”
Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan wasu ƙasashen Turai, ciki har da tsibirin Iberia da Girka da kuma ƙasashen yankin Baltic.
Shugaban Sudan Janar al-Burhan ya gana da gwamnatin Amurka a ɓoye, in ji wani rahoto.
Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar don kamo jagoran ‘yandaban Haiti.
Sources
1. Premium Times Hausa.
2. Aminiya.
3. RFI Hausa.
4. BBC Hausa.
5. Premium Times Hausa.
source