Kwana 70 da ƙaddamar da taraktoci 2,000 na gwamnati har yanzu manoma ba su ga komai ba
[ad_1]
Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana.
Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba.
Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas (NEGF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin kayayyakin noman damina da na rani.
Taron ƙungiyar da ya gudana a Jalingo, Jihar Taraba a ƙarshen makon jiya, ya bayyana cewa tsadar kayayyakin noma da matsalar jinƙai na ƙara tsananta barazanar ƙarancin abinci.
Gwamnonin sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin noman rani tare da tabbatar da kayan aikin sun isa ga manoma ba tare da jinkiri ba.
Yadda aka ƙaddamar da kayan aikin noman
A ranar 24 ga watan Yuni, 2025, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin injinan noma a ƙarƙashin Shirin Fata Sabon Gobe, inda aka kawo taraktoci 2,000 daga ƙasar Belarus tare da kayan gyara, injinan girbi da sauransu.
Gwamnati ta ce za a yi amfani da taraktocin wajen noma hekta 550,000 da samar da ayyukan yi 16,000 da kuma taimaka wa iyalan manoma fiye da dubu 550.
Sai dai bincikenmu ya gano cewa har yanzu taraktocin suna an a ajiye a Cibiyar Hukumar Inganta Irin Noma ta Kasa (NASC) da ke Abuja.

Manoma na ƙorafi
Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim, ya ce: “Abin mamaki ne har yanzu ba a raba taraktocin ba. Muna riƙon gwamnati ta hanzarta raba su ta hanyar da ta dace domin kada daminar bana ta wuce.”
Haka ma Dakta Ogbo Douglas, shugaban Kungiyar Manoma Maso Rajin Ci-gaban (AFPA), ya bayyana jinkirin a matsayin “abin takaici.”
Izinin Fadar Shugaban Ƙasa muke jira — Minista
Wasu manyan jami’an Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya sun shaida wa Wakilinmu cewa an gama tsara yadda za a raba taraktocin jiha-jiha, amma ana jiran sahalewar Fadar Shugaban Ƙasa.
Ministan Aikin Gona, Sanata Abubakar Kyari, ya ce, “Za mu tabbatar da cewa taraktocin za su yi aiki sosai ba wai a ajiye kawai ba. Da zarar mun samu izini, za mu fitar da tsarin farashin da zai zama mai sauƙi ga manoma,” in ji shi.
A baya ma an sha yi wa manoma irin wannan alƙawarin amma ba tare da an cika ba.
A 2018, an yi alƙawarin kawo taraktoci 10,000 daga kamfanin John Deere, sannan a 2021 aka ce za a kawo taraktoci 60,000, amma ba a aiwatar ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link