Kwamishinoni da Shugabannin Ƙananan Hukumomi sun goyi bayan sauya sheƙar Abba zuwa APC

[ad_1]



’Yan majalisar dokokin jiha na jam’iyyar NNPP, shugabannin ƙananan hukumomi 44 da kwamishinoni sun bayyana goyon bayansu ga sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya tabbatar wa wakilinmu cewa gwamna Abba Kabir Yusuf tare da shugabannin ƙananan hukumomi da kwamishinoni za su shiga APC nan ba da jimawa ba.

Rurum ya ce ya gana da gwamnan a ranar Lahadi, inda suka tattauna kan shirin sauya sheƙar, kuma nan ba da jimawa ba za a karɓe su a APC.

Da aka tambaye shi ko gwamnan zai sauya sheƙa tare da jagoransa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Rurum ya ce: “A duk tattaunawarmu ba mu taɓa yin magana kan Kwankwaso ba. Mun tattauna kan dabarun sauya shekar Gwamna Abba, amma ba mu taɓa yin magana kan sauya sheƙar Kwankwaso ba.”

’Yan Majalisa sun goyi baya

Aminiya ta gano cewa banda mutum uku, dukkan sauran ’yan majalisar NNPP na Kano za su sauya sheƙa tare da gwamnan.

Wata majiya ta ce ’yan majalisar za su gana da gwamnan yau domin bayyana goyon bayansu ga sauya sheƙar.

Matsayin Kwankwaso

Sai dai wata majiya kusa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta shaida wa wakilinmu cewa jagoran Kwankwasiyya bai goyi bayan sauya sheƙar ba.

A cewar majiyar, yayin da Gwamna Abba ke ci gaba da tuntuɓa da manyan jiga-jigan APC kan shirin sauya sheƙarsa, Kwankwaso kuma yana ƙoƙarin dakatar da wannan mataki.

“Ina ganin shi ne dalilin da ya sa shugaban NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya yi jawabi ga manema labarai yana nesanta jam’iyyar daga wannan mataki.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *