Jirgin sojojin sama ya kashe mamoma 2 ‘bisa kuskure’ a ƙauyen Neja

[ad_1]



Aƙalla manoma biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama ciki har da ƙananan yara suka jikkata a harin sama da aka kai garin Kurgi da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa wani jirgin sama mai bincike, wanda ake zargin na rundunar sojin saman Najeriya ne, ya yi ta shawagi a sama na tsawon mintuna a ranar Lahadi kafin ya fara harbi kan mutanen da ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Wani mazaunin yankin ya ce harsashin ya afka wa mazauna yankin har cikin gidajensu, inda ya rutsa har da yara a cikin wadanda ya jikkata.

Wani mazaunin yankin, Suleiman Sanusi, ya ce lamarin ya jefa al’umma cikin tsoro, inda da dama suka tsere zuwa garin Bangi da wasu wuraren da suka fi aminci.

Ya bayyana harin a matsayin abin mamaki da kuma na ba-zata.

Sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike cikin gaggawa da kuma samar da taimakon lafiya ga wadanda suka jikkata.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin saman Najeriya da sauran hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *