Iran ta kai hari ma’ajiyar makaman Amurka da ke Iraƙi

[ad_1]



Ƙasar Iran ta sake kai wani sabon hari ma’ajiyar makaman Amurka da ke sansanin sojojinta na Erbil a ƙasar Iraƙi.

Zuwa yanzu dai Iran ta kai hare-hare kan aƙalla sansanonin sojin Amurka guda shida a sassan Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai mata farmaki a ranar Asabar, kamar yadda binciken jaridar New York Times ya nuna.

Rahoton ya ce ba a kai ga tantance adadin makaman da Iran ta harba ko nawa aka daƙile ba, sai dai hare-haren sun jefa ayar tambayoyi kan irin kariyar da waɗannan sansanoni ke da ita nan gaba.

Bayanai sun ce an kai hare-hare a Bahrain, Iraƙi, Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa, da kuma wurare uku a Kuwait a ranakun Asabar da Lahadi, inda aka lalata gine-gine da kayan sadarwar tauraron ɗan Adam.

Jami’an Amurka sun ce sojoji uku sun mutu, biyar kuma sun jikkata sosai a harin da aka kai sansanin Arifjan da ke Kuwait.

Daga cikin wuraren da aka kai hari har da hedikwatar Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka ta Biyar a Manama, sansanonin soji, filayen jiragen sama, da wurin shakatawar sojojin ruwa a Tashar Jebel Ali.

Haka kuma, hare-haren sun yu ɓaran a Ali Al Salem Air Base da sansanin soji a filin tashi da saukar jirage na Erbil.

Bidiyo da hotunan tauraron ɗan Adam sun nuna tashin gobara da rugujewar gine-gine a wasu wuraren, lamarin da ke ƙara nuna tsananin hare-haren da aka kai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *