HOTUNA: Shugabannin ADC sun dira Kano gabanin sauya sheƙar Kwankwaso
[ad_1]
Manyan shugabannin jam’iyyar ADC (African Democratic Congress) sun isa Kano a ranar Litinin, gabanin sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, zuwa jam’iyyar.
Tawagar, wadda ta ƙunshi fitattun ‘yan siyasa, ta sauka a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, inda tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tarbe su.
Daga cikin manyan jagororin da suka sauka a birnin na Dabo akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma shugaban ADC na ƙasa, David Mark; sakataren jam’iyyar na ƙasa, Peter Obi; da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Sanata Dino Melaye; tsohon shugaban APC na ƙasa, John Odigie-Oyegun; da tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.
Aminiya ta ruwaito cewa, kai tsaye tawagar ta wuce gidan Kwankwaso da ke Miller Road a unguwar Bompai, inda ake ci gaba da shirye-shiryen ƙarshe na sanar da sauya sheƙarsa zuwa ADC a hukumance.

Masu alaƙa
[ad_2]
Source link