Category: Latest News

  • Gadar Da Sin Ta Gina Ta Inganta Yawon Bude Ido A Tsibirin Kasar Mozambique

    [ad_1]

    Shugaban Mozambique Daniel Francisco Chapo, ya halarci bikin kaddamar da wata gada da aka gina cikin ruwa a tsibirin Inhaca dake gabar ruwa ta Maputo a jiya Juma’a. Kamfanin gine ginen tituna da gadoji na kasar Sin, CRBC ne ya gudanar da aikin gadar.

    Tsibirin Inhaca mai tazarar kilomita 30 daga Maputo babban birnin kasar, na da kimanin mazauna 6,000 kuma ya yi fice ne saboda albarkatun yawon bude ido. A baya, ruwa mara zurfi dake kewayen tsibirin ya hana jiragen ruwan jigilar fasinja isa bakin tsibirin kai tsaye, lamarin dake tilasta wa fasinjoji komawa kananan kwale-kwale.

    Sabuwar gadar mai tsayin kilomita 1.3, na ba jiragen ruwan fasinjoji damar tsayawa a bakin tsibirin karkashin ko wane yanayi. Kuma yanzu, masu ziyara na iya kai wa tsibirin kai tsaye ta hanyar amfani da gadar, lamarin da ya kyautata tsaro da ingancin sufurin fasinjoji. (Mai fassara: FMM)

    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji Sun Ƙwato Dabbobi 257 Da Aka Sace A Kano

    [ad_1]

    Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa a Gwarzo, ƙarƙashin jagorancin jami’an 3 Brigade, Nigerian Army na Sojojin Nijeriya, sun daƙile wani yunƙurin satar shanu a Jihar Kano, inda suka ceto dabbobi 257.

    Wannan aikin ya biyo bayan kiran gaggawa da aka samu da safiyar Lahadi, kimanin ƙarfe 6:57 na safe, inda aka bayar da rahoton cewa ’yan fashi sun sace shanu daga ƙauyen Mainika a Ƙaramar Hukumar Gwarzo.

    • Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Biyayyar Siyasa A Rundunar Sojoji Domin Bunkasa Zamanantar Da Tsaron Kasa
    • Kiwon Awakan Alfarma Na Ƙara Haɓaka A Jihar Kano

    A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Mataimakin Darakta na Hulɗa da Jama’a na Sojojin Ƙasa, 3 Brigade, Major Babatunde Zubairu, ya ce sojojin sun tashi cikin sauri zuwa wata hanyar da ake zargin ’yan fashi suna bi, inda suka tare ’yan fashin da ke gudu a ƙauyen Dayi.

    “Da safiyar 1 ga Maris, 2026, kimanin ƙarfe 0657 na safe, sojojin JTF, a martani ga kiran gaggawa, sun tashi cikin sauri zuwa wata hanyar da ake zargin ’yan fashi suna bi, suka yi nasarar tare da yaƙi da wani rukuni na ’yan fashi masu makami a ƙauyen Dayi, waɗanda suka sace shanu daga ƙauyen Mainika a baya.

    “Da suka haɗu da sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa, ’yan fashin sun gudu cikin hargitsi zuwa Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, suka bar dabbobin da suka sace, waɗanda sojojin suka ceto cikin nasara,” kamar yadda wani ɓangare na sanarwar ya bayyana.

    Dabbobin da aka ceto sun haɗa da shanu 135, tumaki 119, akuya 1 da jakuna 2, jimillar dabbobi 257.

    “An miƙa dabbobin da aka ceto, wanda ya haɗa da shanu 135, tumaki 119, akuya 1 da jakuna 2, jimillar dabbobi 257, ga masu su ta hanyar hukumomin ƙasa,” a cewar sanarwar.

    Sojojin sun ce ’yan fashin sun sami mummunar asara yayin yaƙin.

    “’Yan fashin sun yi mummunan asara yayin yaƙin,” in ji sanarwar.

    Rundunar Haɗin Gwiwa a Gwarzo ta haɗa sojojin 3 Brigade na Sojojin Nijeriya, ‘Nigeria Police Force, Department of State Serɓices’, Nigeria Security and Ciɓil Defence Corps’, da masu sa ido na ƙasa.

    Kwamandan 3 Brigade, Soja Janar Ahmad Tukur, ya yaba da jarumtaka, ƙarfin hali da ƙwarewar sojojin, inda ya ce ƙwarin gwiwa da ruhin yaƙinsu na da ƙarfi.

    Ya kuma gode da goyon bayan al’umma wajen bayar da muhimman bayanai da suka kai ga nasarar aikin.

    “Har zuwa lokacin fitar da wannan sanarwar, lamarin yana ƙarƙashin iko, yayin da ake ci gaba da sa ido don hana aukuwar wasu lamurra.

    “An umarci rundunar da ta ci gaba da ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da tsaron yankin don kare rayuka da dukiyoyi,” a cewar sanarwar.

    [ad_2]

    Source link

  • An kammala kaɗa ƙuri’ar zaɓen magajin Khamenei

    [ad_1]



    Majalisar ƙoli ta malaman addini da ke da alhakin zaɓen sabon jagoran ƙasar Iran ta ce ta riga ta yanke hukunci kan wanda zai gaji kujerar, amma har yanzu ba a bayyana sunansa ba.

    Mamba a cikin majalisar, Ahmad Alamolhoda, ya ce an riga an kaɗa ƙuri’ar zaɓen sabon jagoran, kuma an cimma matsaya kan wanda zai hau kujerar.

    Sai dai ya ce sakatariyar majalisar ce za ta sanar da sunan wanda aka zaɓa nan gaba.

    Wasu mambobin majalisar sun tabbatar da cewa an riga an yanke shawara, inda ɗaya daga cikinsu ya nuna yiwuwar ɗan marigayi jagoran ƙasar, Mojtaba Khamenei, zai gaji kujerar mahaifinsa.

    Mojtaba dai ɗan Ali Khamenei ne, wanda ya zama jagoran ƙasar tun shekarar 1989.

    Muƙamin jagoran addini na Iran shi ne mai mafi girman iko a harkokin siyasa da addini a ƙasar, kuma shi ne ke da ikon yanke hukunci kan muhimman batutuwan gwamnati.

    Wani mamba na majalisar daga lardin Khuzestan, Mohsen Heydari, ya ce mafi dacewa daga cikin ‘yan takarar ne aka zaɓa bayan samun rinjayen ƙuri’u.

    A bayan nan dai Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha nanata cewa yana son ya taka rawa wajen zaɓen sabon jagoran, inda kuma ya yi watsi da yiwuwar Mojtaba Khamenei ya gaji kujerar, yana mai cewa bai cancanta ba.

    Sai dai jami’an Iran sun yi watsi da wannan batu, suna mai cewa Amurka ko wata ƙasar ba ta da wani tasiri a kan zaɓen sabon jagoran ƙasar.

    Aminiya ta ruwaito cewa marigayi Ayatollah Ali Khamenei ya mutu ne a ranar 28 ga Fabrairu bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran, lamarin da har kawo yanzu ke ci gaba da rura wutar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Tarihin muƙamin jagoran addini na Iran

    Mutumin da ya fi kowa iko a Iran shi ne jagoran addinin ƙasar tun bayan juyin juya-halin ƙasar da aka yi a 1979 da aka hamɓarar da mulkin sarauta ta Mohammad Reza Pahlavi.

    Zuwa yanzu ƙasar ta yi jagororin addini guda biyu — Ayatollah Ruhollah Khomeini (wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci a ƙasar) sai wanda ya gaje shi, marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

    Shi ne jagoran ƙasa kuma babban kwamandan tsaron ƙasar. Yana da iko a kan rundunar ’yan sanda da kuma jami’an Hisbah na ƙasar.

    Jagoran addinin ne kuma yake da iko a kan dakarun juyin juya-hali ta ƙasar, wadda ita ce rundunar da ke kula da harkokoin tsaro na cikin gida, tare kuma da ɓangarenta na sojojin sa-kai da ake kira Basij.


    [ad_2]

    Source link

  • An Dakatar Da Kocin Manchester City Pep Guardiola Daga Buga Wasanni Biyu

    [ad_1]

    Mahukuntan gasar Firimiya ta kasar Ingila sun dakatar da kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola daga buga wasanni biyu da suka hada da wasan da zasu buga da West Ham United a gasar Firimiya da kuma wasan zagayen na kusa da na karshe na gasar FA Cup da zasu buga a watan Afirilu.

    Hakan ya biyo bayan katin kora da ya samu a wasan da Manchester City ta doke Newcastle United da ci 3-1 a gasar cin kofin FA da suka buga ranar Asabar, wannan ne karo na shida da aka bai wa Guardiola katin gargadi a wannan kakar, lamarin ya faru ne bayan da tsohon kocin na Barcelona ya yi cacar baki da alkalin wasa na hudu, Lewis Smith bayan da Kieran Trippier ya yi wa Jeremy Doku na City keta.

    Yanzu kenan Guardiola ba zai halarci wasan kungiyar da West Ham a filin wasa na London Stadium a gasar Premier ranar Asabar mai zuwa ba da kuma wasan kusa da na karshe na gasar FA a watan Afrilu, duk da haka dakatarwar ba ta shafi wasannin gasar zakarun Turai ba, don haka za a bar Guardiola ya shiga filin wasa a wasan da zasu buga da Real Madrid a gasar zakarun Turai da kuma wasan karshe na Carabao da zasu buga da Arsenal a ranar 22 ga watan Maris.

    [ad_2]

    Source link

  • Trump ya halarci bikin karɓar gawarwakin sojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran

    [ad_1]



    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya halarci bikin karɓar gawarwakin sojojin Amurka shida na farko da suka mutu a rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Amurka da Iran.

    An sauke gawarwakin sojojin ne ranar Asabar a sansanin sojin sama na Dover, inda ake karɓar gawarwakin sojojin Amurka da suka mutu a ƙasashen waje kafin a kai su wajen shirya jana’iza.

    Trump ya yi gaisuwar karramawa tare da sarawa yayin da sojoji ke sauke akwatunan gawarwakin da aka rufe da tutar Amurka daga jirgin soji.

    Shugaban ya samu rakiyar uwargidansa Melania Trump, da mataimakin shugaban kasa, JD Vance, da Sakataren Tsaro, Pete Hegseth, da shugaban hafsoshin sojojin Amurka Dan Caine, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

    Rahotanni sun ce sojojin shida — maza biyar da mace guda — sun mutu ne a ranar Lahadi bayan wani jirgin yaƙi maras matuƙi ya kai hari kan wani muhimmin sansanin sojin Amurka a Kuwait.

    Lamarin ya faru ne kwana guda bayan da Amurka tare da Isra’ila suka ƙaddamar da manyan hare-haren soji kan Iran.

    Sojojin da suka mutu mambobi ne na rundunar ajiyar soji ta 103rd Sustainment Command da ke hedikwata a Des Moines, wadda ke da alhakin samar wa sojoji abinci, mai, kayan aiki da alburusai.

    Karɓar gawarwakin sojojin Amurka — wanda ake kira dignified transfer — na ɗaya daga cikin muhimman al’adu na soji da shugaban Amurka kan halarta domin girmama waɗanda suka mutu a bakin aiki.

    Harin da ya kashe sojojin ya ƙara nuna haɗarin da sojojin Amurka ke fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da Iran ke ci gaba da harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan sansanonin Amurka da ƙawenta a yankin.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai wa Iran hare-hare masu tsauri kuma za ta faɗaɗa hare-haren zuwa wasu sabbin wurare idan rikicin ya ci gaba da tsananta.


    [ad_2]

    Source link

  • Trump ya zargi Iran da kai hari makaranta a Kudancin ƙasar

    [ad_1]



    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Iran da kai harin da hukumomin ƙasar suka ce ya afka wa wata makarantar firamare ta ‘yan mata a kudancin ƙasar.

    Trump ya bayyana haka ne ga manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, inda ya ce suna zargin Iran ne saboda yadda makaman da take amfani da su ba su da cikakken daidaito.

    “Muna tunanin Iran ce ta kai harin da kanta, saboda makaman da take amfani da su ba da nagarta da ingancin kai hari kan ainihin inda suka nufa,” in ji Trump.

    Rahotanni daga hukumomin Iran sun ce harin ya auku ne a wata makarantar firamare ta ‘yan mata a yankin Minab, inda aka ce sama da mutum 150 suka mutu, yawancinsu dalibai.

    Sai dai har yanzu babu wata ƙasa da ta ɗauki alhakin harin. Amurka da Isra’ila sun ce har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin, yayin da Iran ke zargin ƙasashen biyu da hannu a kai.

    Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce bai samu damar kai ziyara wurin da abin ya faru ba domin tabbatar da lamarin, haka kuma babu tabbacin adadin waɗanda suka mutu daga wata majiya mai zaman kanta.

    A wani ɓangare, dakarun juyin-juya hali na Iran IRGC sun ce sun kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al Dhafra da jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami, suna zargin cewa an yi amfani da sansanin wajen kai harin.

    Ma’aikatar tsaron Amurka, ta tabbatar da cewa ana binciken lamarin, yayin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce Amurka ba za ta kai hari da gangan kan makaranta ba.

    Jaridar The New York Times ta rawaito cewa bayanan sojojin Amurka na nuna cewa hare-haren da ake kai wa kan wasu wuraren sojin ruwa kusa da Mashigar Hormuz na iya kasancewa suna da alaƙa da harin da ya afka wa makarantar.


    [ad_2]

    Source link

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 19

    [ad_1]

    Fa’idar Sahur

    1. Yin sahur koyi ne da annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam), kuma malamai sun yi ijma’i a kan mustahabbi ne yinsa kamar yadda Ibnul Munzir da Imamu Annawawi suka naƙalto.

    2. Yin sahur saɓa wa Yahudu da Nasara ne, domin su ba sa yin sahur a azuminsu kamar yadda Muslim da Abu Dawud Tirmizi da Nasa’i suka ruwaito.

    • Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana
    • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 10

    3. Sahur albarka ne ga mai yinsa kamar yadda hadisi ya gabata.

    4. Sahur yana samar da karfi ga mai azumi wajen yin ibada, da kuma ƙaruwar nishadi, da kuma tunkuɗe mummunar dabi’a da yunwa take haifarwa. Kuma a lokacin yinsa sahur, mutum yana samun dama ya yi sadaƙa ga almajiri ko kuma su ci tare. kuma yana sa mutum ya yi zikiri da addu’a, domin lokacin ne da ake karbar addu’a… “kamar yadda Hafiz Ibnu Hajar ya bayyana a littafinsa Fathul Bari (4/496) da malaminsa Ibnu Mulaƙƙin a cikim  al’I’ilamu (5/187)

    5. Samun salati daga Allah da mala’ikunsa.

    Allah ya datar da mu ga koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) a cikin al’amuranmu baki daya.

    [ad_2]

    Source link

  • Illolin Tsarki Da Sabulu Ga Mace

    [ad_1]

    Bisa kyakkyawan zato, mafi yawan mata kan yi tsarki da sabulu ne da manufar tsaftace jikinsu, sai dai, kash, rashin sani ya sa su ke aikata hakan, domin da sun san irin lahanin da ya ke mu su da ba su yi tsarki da sabulu ba.

    Wani ƙwararren likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan, Imran Morhason-Bello, ya ce, wasu abubuwa da mata ke aikata wa cikin rashin sani, kamar amfani da turare ko sabulu a gaba, na sa su kamuwa da cota.

    • Manyan Jami’o’in Kasar Sin Sun Samar Da Karin Guraben Karatu 38,000 Cikin Shekaru Biyu Da Suka Gabata
    • CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

    Saboda da haka sai Likita ya shawarci ‘yan uwa mata kan su guji yin amfani da sabulu ko turare a gabansu da nufin tsaftace wajen, don kuwa a maimakon gyara hakan na iya janyo mu su mummunar illa, inda zai haifar da rashin jin daɗin.

    Dokta Morhason-Bello, ya ba da wannan shawara ne a wata makala da ya gabatar wajen wani taro da aka gudanar da nufin dakile al’adar yi wa mata kaciya a Najeriya.

    Taron, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta shirya tare da taimakon Ƙungiyar (UNPFA) ta majalisar ɗinkin Duniya, da Jami’ar Ibadan ta gudanar da shi ne a birnin tarayyar ƙasar nan, Abuja.

    Kwararren likitan ya bayyana cewa, ba kaciyar mata ce kawai ke haifar da mummunar illa ga al’aurar mata ba wajen jin gyara mace, har ma da amfani da sabulu ko turare da mata ke yi da nufin tsaftace al’aurarsu ko kuma amfani da wasu magungunan kayan mata.

    Ya ce, lokacin da mace ta saba da yin amfani da sabulu ko turare wajen tsaftace gabanta, ko kuma yin amfani da magungunan kayan mata, to sannu kan hankali hakan zai yi tasiri a gabanta, sannan daga bisani sai ya yi mata mummunar illa ta hanyar haifar mata cuta

    A cewarsa, “fatar jikin dan-tsakan mace da ta tsakiya jikinta ba ta da kauri, kuma cike suke da jijioyoyin jini ma su yawan gaske, sakamakon yawan amfani da sabulu ko turare ko kuma kayan mata da mata ke yi, sai fatar ta dunƙule ta gaza kai sako ga kwakwalwa a karshe sai hakan ya haifar wa da mace cutar ciwon sanyi.

    Dokta Morhason-Bello ya ƙara da cewa, domin ƙubuta daga wannan matsala, dole ne mata su guji cusa magungunan kayan mata, ko kuma sanya magungunan zamani ba tare da iznin likita ba, hakanan su guji yin amfani da turare, ko sabulu, saboda hakan zai hana su sakewa, baya ga haka ma zai iya haifar mu su da cututtuka.

    “A gaskiya, wasu daga cikinsu na amfani da hannayensu wajen cusa waɗannan magungunan cikin jikinau , abin da ba su sani ba shine, idan su ka ɗauki tsawon lokaci su na aikata hakan, sai ya haifar mu su da matsewar jikinsu fiye da kima. Mun sha samun matsalolinan.

    “Idan mace ta samu kanta cikin wannan matsala, don warkar da ita akwai buƙatar a yi ma ta aikin tiyata nau’i daban-daban ko kuma ayi koƙarin samar ma ta da wata saban waje. Kafin a samu nasarar hakan kuma dole matar ta zauna a asibiti tsawon watanni ma su yawa.

    “Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga mace don tsaftace jikinta shine ruwa mai tsabta kawai. Idan ta yi amfani da duk wani abu da yake ɗauke da wani sanadari kamar sabulu ko turare, zai iya kashe kwayoyin halittar da Ubangiji ya halitta mata don jikinta ya zauna lafiya.

    Amma yayin da ta lahanta ƙwayoyin halittar da Ubangiji ya yi mata, sai ƙwayoyin cuta su samu damar shiga jikinta. A ƙarshe irin waɗannan mata za su fara fitar da gurbataccen ruwa, “inji shi.

    Ya ci gaba da bai wa mata shawarar cewa, kama ta ya yi su ke wanke jikinsu da ruwa mai tsafta kaɗai, kuma “kar mata su damu da wani wari da ke fita daga jikinsu saboda wannan warin dabi’ar da Allah Ya halicci wajen ne, matuƙar ba wari ne na cuta ba, wanda shi kuma warin cuta ya na kasancewa mai yawa ne”.

    [ad_2]

    Source link

  • Daftarin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Karo Na 15 Ya Shaida Raya Sabbin Sha’anin Kasar

    [ad_1]

    A yau Asabar 7 ga wata, shugaban sashen kirkire-kirkire da fasahohin zamani, na kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Bai Jingyu, ya bayyana a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin cewa, daftarin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, ya shaida tsarin raya sha’ani daban daban, da kafa tsarin raya sabbin sha’ani bisa manyan tsare-tsare da hangen nesa.

    A halin yanzu, ya kamata a ci gaba da raya sabbin sha’ani, kamar fasahohin sadarwa da sabbin makamashi da sauransu, da raya tsarin sha’ani bisa yanayin da ake ciki, da amfani da fifikonsu yadda ya kamata.

    Har ila yau, za a yi kokari wajen raya sabbin sha’ani masu muhimmanci, kamar su kirar matattarar bayanai ta microchip, da kimiyyar kiwon lafiya, da binciken sararin samaniya da sauransu, don raya su zama sabbin jigon raya tattalin arzikin kasar.

    A nan gaba kuma, za a maida hankali ga sabbin sha’ani kamar su fasahohin Quantum, da fasahohin hada kwakwalwa da na’urori, da fasahohin mutum-mutum inji da sauransu, don raya su a matsayin jigon sha’ani na nan gaba. (Zainab Zhang)

    [ad_2]

    Source link

  • NPA Ta Ce Jiragen Ruwa 33 Ɗauke Da Kaya Sun Sauka A Tashohin Legas

    [ad_1]

    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA, ta sanar da cewa, Jiragen Ruwa guda 33 ɗauke da Man Fetur da kayan abinci da kuma sauran wasu kaya, sun sauka a Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa, Tin-Can Island da kuma Lekki Deep Sea da ke a jihar Legas.

    NPA ta bayyana haka ne, a cikin sanarwar da ta saba fitarwa a kullum, wanda Hukumar ta ce ana sa ran Jiragen sun sauka ne daga ranar 2 zuwa ranar 8 na wannan watan.

    • NPA Ta Samu Ƙaruwar Kashi 24.8 Na Kayayyakin Da Ke Shigowa Daga Ƙasashen Waje
    • Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri

    A cewar sanawar daga cikin Jirage 16 na ɗauke da kaya iri da ban da bana da suka haɗa da, Buhuhunan Takin samfarin urea, ɗanyen Mai, Gishiri da Ɗinbin Buhuhun takin zamani da sanadaran, gypsum, da Buhuhun Suga da sauransu.

    A wata sabuwa kuma, Hukumar ta NPA, ta bayyana cewa, tuni wasu Jiragen Ruwa guda 11, ɗauke da man dizil da fetir da sauransu suka sauka a Tashoshin.

    Kazalika, Hukumar ta sanar d acewa, wasu Jiragen Ruwa guda 17 a yanzu haka, sun sauke kayan da suka haɗa da, Taken urea, Buhuhunan Alkama, Gas da wasu kwantainoni, suka sauka a Tashoshin Tincan, Apapa, da kuma Lekki.

    [ad_2]

    Source link