Benin Ta Gudanar Da Bikin Ranar Taijiquan Ta Duniya A Karon Farko
[ad_1]
An gudanar da hidindimu da sauran harkoki na gabatarwa jiya Asabar a Godomey mai tazarar kilomita 30 daga Cotonou, babban birnin kasar Benin, domin bikin ranar Taijiquan ta duniya karo na farko a kasar.
Cibiyar al’adun kasar Sin da ke kasar Benin ce ta kirkiro da bikin, kuma tawagarta ta Wushu ta shirya, tare da goyon bayan kungiyar Wushu ta ‘yan asalin kasar Benin. Wanda ya kunshi gudanar da hidindimu kai-tsaye, da koyarwa da cudanya da juna, bikin ya samu mahalarta fiye da 100, ciki har da ‘yan kasa da dalibai daga Cibiyar Confucius a Jami’ar Abomey-Calavi.
Jakadan bunkasa Wushu na Sin da Benin, Fabrice Noudofinin, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, “Bikin na ranar Taijiquan ta duniya, na da nufin inganta al’adun Taijiquan ne, da wayar da kan jama’ar kasar Benin game da fa’idodin kiwon lafiyarsu, da inganta mu’amalar al’adu, da karfafa huldar dake tsakanin kasashen Benin da Sin.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link