Babban Editan LEADERSHIP, Azu, Ya Samu Lambar Yabo Ta NUJ Kan Ƙwarewar Aikin Jarida
[ad_1]
Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen Babban Birnin Tarayya (FCT), ta zabi Babban Editan jaridar LEADERSHIP, Azu Ishiekwene, domin karbar lambar yabo ta ‘Media Leadership Excellence Award’ ta shekarar 2026.
An tsara wannan taron bayar da lambar yabo ne domin girmama ‘yan jarida da suka yi fice wajen nuna kwarewa, gaskiya, da kuma jajircewa wajen kiyaye ka’idojin aikin jarida mafi inganci.
- Taɓarɓarewar Sabis: NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Biya Diyya
- Tinubu Ya Ware Albashinsa Don Tallafa Wa Sojoji Da Iyalansu
A cikin wasikar nadin da Shugabar NUJ ta FCT, Grace Ike, da Shugaban Kwamitin Tsare-tsare, Obas Esiedesa, suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana cewa an yi la’akari da kwarewar aiki, shaharar masana’antar yada labaran, da kuma tasirin aikin jarida ga al’umma wajen zaben wanda zai samu kyautar.
A cewar NUJ, an zabi Azu ne saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a aikin jarida, jajircewarsa wajen bin ka’idojin da’a, da kuma kokarinsa na yada labarai masu inganci, masu daidaito, kuma masu tasiri.
Wannan lambar yabo na daga cikin shirye-shiryen bikin Makon Jaridu na NUJ FCT na 2026, wanda za a gudanar a ranar Talata, 19 ga Mayu, 2026, a Abuja.
Ishiekwene na da kusan shekaru 40 yana aikin jarida. Mamba ne a Nigerian Guild of Editors (NGE), kuma ya taba zama shugaban kwamitin tantancewa na kyautar bayar da kyaututtuka ga hazikan ‘yan jarida na Afirka (CNN African Journalists of the Year).
Yana daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Hadin Kan Editoci na Duniya (GEN), sannan ya taba zama mamba a kwamitin Dandalin Editoci na Duniya (WEF), kuma yana daga cikin fitattun marubutan sharhi a Afirka.
Ya rubuta littattafai da dama, ciki har da sabbi guda biyu da aka wallafa kwanan nan — ‘Writing for Media and Monetising It’, da ‘A Midlifer’s Guide to Content Creation and Profit’.
Haka kuma, shi ne shugaban Openfees, wata kungiya mai zaman kanta da ke biyan kudin makaranta ga daliban firamare da sakandare marasa galihu a Abuja.
Ya lashe lambobin yabo da dama, sannan yana koyarwa a matsayin dan sa-kai a tsohuwar makarantar sa, Sashen Mass Communication na Jami’ar jihar Legas.
[ad_2]
Source link