An Tsare Shugaban KANSIEC Da Wasu Biyu A Gidan Yari Bisa Zargin Karkatar Da Kuɗi Naira Biliyan 1
[ad_1]
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Talata ta ba da umarnin a tsare Sani Malumfashi, shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano KANSIEC, da wasu biyu a gidan yarin Kuje bisa zarginsu da laifin almundahanar kudi har Naira Biliyan 1.
Mai Shari’a, James Omotosho ya bayar da umarnin ne bayan Malumfashi da waɗanda ake ƙara tare suka musanta zargin aikata laifuka shida da Hukumar Kula da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ta gurfanar da su.
Malumfashi da waɗanda ake ƙara tare, za a tsare su a gidan yarin har sai an kammala sauraron ƙarar da kuma yanke hukunci kan buƙatar belin da suka shigar.
Waɗanda ake ƙara tare da Malumfashi su ne sakataren KANSIEC, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, mataimakin darakta a sashen asusun hukumar zaɓen.
[ad_2]
Source link