An Kashe Ƴan Ta’adda 500 A Hare-haren Ngoshe Da Fatori – Zulum
[ad_1]
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce an kashe ‘yan Boko Haram da ISWAP sama da 500. Ya bayyana hakan ne bayan hare-haren Ngoshe, da Pulka da Malam Fatori da suka faru kwanan nan.
Zulum ya yi wannan bayani ne a Pulka ranar Lahadi yayin rabon tallafi ga waɗanda abin ya shafa. Ya ce duk da asarar da aka yi, an samu manyan nasarori a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda.
- Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno
- Harin Bam A Maiduguri: Har Yanzu Akwai ’Yan Ƙunar Baƙin Wake Biyu Da Suka Yi Ɓatan Dabo – Zulum
Ya jaddada cewa ana yawan bayyana munanan labarai ne kawai ga jama’a. Ya ce ya kamata a riƙa bayyana nasarorin da sojoji ke samu a fagen daga.
Gwamnan ya yabawa rundunar soji da ta sama bisa ƙoƙarinsu a yaƙin. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kuɗaɗe don ƙarfafa MNJTF a yankin Mandara.
Zulum ya ce al’ummar Borno ba za su yi kasa a gwuiwa ba duk da hare-haren. Ya ƙara da cewa za su ci gaba da fafutukar kawo zaman lafiya da doke ‘yan ta’adda.
[ad_2]
Source link