An kama wanda ya kashe ɗan uwansa ya binne shi
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta kama wani mutum mai shekara 35, Chukwudalu Ezeani bisa zargin kashe ɗan uwansa, Chinedu Ezeani, sannan ya binne gawarsa a wani rami marar zurfi a ƙauyen Afube da ke Amichi, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar.
Wanda ake zargin ya aikata wannan ɗanyen aikin ne a ranar 1 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 8 na dare a gidansa, kafin ya boye gawar a cikin gidansa na tsawon kusan watanni takwas.
Kakakin rundunar’yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana cewa tun farko an kai rahoton ɓacewar mutumin ne a ofishin ’yan sanda na Amichi.
A cewarsa, jami’an sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Awka, daga baya sun sake duba lamarin biyo bayan bayanan sirri da aka samu, wanda hakan ya kai ga kamo wanda ake zargin.
“Jami’an sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) a Awka, sun bankaɗo wani lamari na ɓacewar mutumin da ya shafe watanni takwas ta hanyar kama wani Chukwudalu Ezeani, mai shekara 35, dangane da kisan ɗan uwansa, Chinedu Ezeani, mai shekara 52,” in ji Ikenga.
“Binciken farko ya nuna cewa a ranar 1 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 8 na dare, wanda ake zargin ya kashe mamacin a gidansa da ke ƙauyen Afube, Amichi, sannan ya binne gawar a wani rami marar zurfi a cikin filin gidansa, ta yadda ya boye laifin na tsawon watanni takwas,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link